Sojoji Sun Ragargaza ‘Yan Ta’addan ISWAP Suna Tsaka da Kotun Hada Bama-bamai a Borno

Sojoji Sun Ragargaza ‘Yan Ta’addan ISWAP Suna Tsaka da Kotun Hada Bama-bamai a Borno

  • Dakarun sojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan mayakan ta’addancin ISWAP a yankin tafkin Chadi yayin da ake koya musu hada bama-bamai
  • Sojin sun kai samame ta jiragen yaki ne a Tumbun inda suka saki ruwan wuta har ‘yan ta’addan suka nemi tserewa ta kwale-kwake 6 dake gabar ruwan
  • Bayanan tsaro sun nuna cewa ’yan ta’addan suna fitowa ta Mallam Fatori a motocin yaki dauke da makamai, lamarin da yasa sojin suka yi maganinsu

Borno - Luguden ruwan bama-bamai da jiragen yakin sojojin saman Najeriya suka yi ya janyo ajalin ‘yan ta’adda 24 na kungiyar ta’addancin ISWAP.

Sojojin Najeriya
Sojoji Sun Ragargaza ‘Yan Ta’addan ISWAP Suna Tsaka da Kotun Hada Bama-bamai a Borno. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An tattaro cewa, an yi aikin ne a ranar Lahadi a Tumbun Hamma, daya daga cikin wuraren da aka tabbatar da cewa mayakan ISWAP din suna horarwa a yankin tafkin Chadi, kamar yadda Zagazola Makama suka bayyana.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Yi Yayyafin Bama-bamai Kan Yan ISWAP a Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Mayaka Masu Yawan Gaske

‘Yan ta’addan da aka halaka kamar yadda majiyar tsaro ta sirri ta bayyanawa PRNigeria, suna koya iya amfani da makamai tare da hada abubuwa masu fashewa a wurin na tsawon kwanaki shida.

OPHK ta kai samame yankunan Tumbun

A wani cigaba makamancin hakan, jirgin sojin saman Najeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai ta kai samame karo daban-daban a Tumbun dake yankin tafkin Chadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan suna daga cikin ruwan wuta ta jiragen yaki na mayar da martani ga ‘yan ta’addan bayan yunkurin kai farmaki da suka yi kan sojojin kasa dake Mallam Fatori.

Kamar yadda majiya daga rundunar sojin ta sanar, bayanan sirri sun bayyana cewa ‘yan ta’addan suna shiga Mallam Fatori daga Tumbun Fulani kuma suna tafe da motocin yaki, makamai masu yawa da sauransu.

“A don haka ne aka samu daukin sojin sama don dakile wasu tare da mitsike lamurransu.”

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram 5 Sun Gamu Da Ajalinsu a Hannun Sojoji, An Kama Daya Da Ransa a Wata Jihar Arewa

Kamar yadda ya dace, ruwan wutan da aka yi a Tumbun Fulani yayi sanadin lalacewar motocin yaki uku da aka boye a kasan bishiya inda wasu ‘yan ta’addan suka dinga kokarin zuwa wurin wasu kwale kwale 6 a gabar tafkin Chadi amma aka halaka su.

Hakan ne ya kawo nakasu ga duk wani kokarinsu na kai hari kan sojojin.

Soji na kokarin ganin bayan ISWAP

A wasu labari na daban, sojin Najeriya na ta kokarin ganin bayan ta’addanci a fadin kasar nan inda suke kai fada har maboyar ‘yan ta’addan dake Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel