Mayakan ISWAP Da Dama Sun Bakunci Lahira Yayin da Sojoji Suka Sauke Bama-bamai 7 a Kan Yan Ta’addan

Mayakan ISWAP Da Dama Sun Bakunci Lahira Yayin da Sojoji Suka Sauke Bama-bamai 7 a Kan Yan Ta’addan

  • Mayakan kungiyar ta'addanci na ISWAP sun dandana kudarsu a hannun dakarun rundunar sojin sama
  • Jirgin yakin soji ya sauke bama-bamai bakwai a kan ya ta'addan yayin da suke zirga-zirga a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno
  • An tattaro cewa mayakan kungiyar da dama sun rasa rayukansu a harin wanda ya gudana a ranar Lahadi

Borno - Mayakan kungiyar ISWAP da dama sun bakuncin lahira bayan dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi yayyafin bama-bamai a matsugunin yan ta’addan da ke yankin karamar hukumar Damboa ta jihar Borno

Shafin Zagazola ya rahoto cewa rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai sun kai wani samame ta sama a ranar 27 ga watan Nuwamba, inda suka hari wani ayari na yan ta’addan a wani waje mai suna Kau-Shoro’a.

Jirgin yaki
Mayakan ISWAP Da Dama Sun Bakunci Lahira Yayin da Sojoji Suka Sauke Bama-bamai 7 a Kan Yan Ta’addan Hoto: HumAngle
Asali: UGC

Wasu majiyoyin tsaro daga rundunar sojin sama, sun sanar da Zagazola Makama cewa jirgin yakin ya yi nasarar tayar da wata motar hilux da ke jigilar wasu mayaka, inda ya kashe daukacin mutanen da ke cikinta.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Machina Matsayin ‘dan Takarar Yobe ta Arewa

Majiyoyin sun kuma bayyana cewa gawarwakin yan ta’addan sun barbazu a fadin wurin yayin da sauran mayakan da suka tsallake rijiya da baya suka ari na kare.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyar ta sha alwashin cewa rundunar sojin sama da ke yaki tare da sauran rundunonin kasa, za su ci gaba da kai munanan hare-haren kan yan ta’adda a yankin arewa maso gabas.

Dakarun soji sun halaka yan ta'adda hudu a jihar Kaduna

A wani labarin kuma, sojoji da ke yaki da yan fashi a yankin arewa ta yamma sun yi nasarar halaka wasu yan bindiga hudu a yankin Tsohon Gayan da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna

Kamar yadda kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana, dakarun na Operation Forest Sanity sun farmaki yan bindigar ne a kokarinsu na tserewa inda suka bindige biyu kuma suka mutu nan take.

Kara karanta wannan

Babban Nasara: Sojoji Sun Murkushe Yan Bindiga 4 a Wata Jihar Arewa

Biyu sun mutu a gaba sanadiyar raunukan da suka ji a yayin artabu da sojojin, an kuma kwato bindigar AK 47 guda daya, babur da kuma harsasai a samamen wanda ya gudana a jiya Lahadi, 27 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel