Zanga-zanga Ya Barke a Katsina Yayin da Yan Bindiga Suka Bindige Mahaifiyar DPO

Zanga-zanga Ya Barke a Katsina Yayin da Yan Bindiga Suka Bindige Mahaifiyar DPO

  • Yan bindiga na ci gaba da addabar al’ummar yankin arewa maso yammacin kasar musamman mazauna jihar Katsina
  • Mahara sun kashe mahaifiyar wani DPO da kaninsa a yankin Danmusa a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba
  • Al’ummar yankin Danmusa sun fito sun yi zanga-zanga domin nuna fushinsu a kan dauki daya daya da ake ci gaba da yi masu

Katsina - Mazauna garin Danmusa da ke hedkwatar karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina sun yi zanga-zanga kan hare-haren yan bindiga a yankin.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, al'ummar garin Danmusa sun fito tituna ne bayan yan bindiga sun kai wani hari da yayi sanadiyar rasa rayukan mahaifiyar wani DPO da kaninsa.

Katsina
Zanga-zanga Ya Barke a Katsina Yayin da Yan Bindiga Suka Bindige Mahaifiyar DPO Hoto: Punch
Asali: UGC

Majiyoyi sun yi bayanin abun da ya faru

Masu zanga-zangar sun cinnawa wasu gidaje wuta ciki harda na wani tsohon malamin makaranta wanda suka zarga da hada kai da yan bindiga.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Yi Yayyafin Bama-bamai Kan Yan ISWAP a Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Mayaka Masu Yawan Gaske

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har ila yau ana fargabar cewa masu zanga-zangar sun kona fadar hakimin garin, amma dai rahotanni sun ce an zuba jami’an tsaro a yankin.

Wata majiya a garin Danmusa ta fadama Daily Trust cewa yan bindiga sun farmaki mutanen da abun ya ritsa da su sannan suka kashe su a gidansu a safiyar Talata, 29 ga watan Nuwamba.

A cewar majiyar, hakan ya faru ne duk da yarjejeniyar zaman lafiya da ke tsakanin mutanen garin da yan bindigar.

Ya ce:

“Akwai yarjejeniyar zaman lafiya da shugaban karamar hukumar ya shiga inda ake barin yan bindigar su shigo cikin gari su siya duk abun da suke so sannan su tafi hankalinsu kwance, yayin da a nasu bangaren, sun yi alkawarin cewa ba zasu farmake mu ba.
“Amma ina mai sanar da kai cewa wannan yarjejeniyar zaman lafiyar duk karya ce, bai hana su garkuwa da mutane don kudin fansa ba da kuma kashe mutane.”

Kara karanta wannan

Babban Nasara: Sojoji Sun Murkushe Yan Bindiga 4 a Wata Jihar Arewa

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana mutane biyun da aka kashe a matsayin Usman Lawal Karzaje, kanin DPOn Yan sanda a karamar hukumar Dutsi da mahaifiyarsu.
“Kafin yanzu, duk da yarjejeniyar zaman lafiya, sun yi garkuwa da Alhaji Rabe Mainadi, bayan sun karbi kudin fansarsa, sun karya masa kafada, har yanzu bai farfado daga wannan ba.
“Abu na biyu, sun yi garkuwa da dan Alhaji Mani, sun karbi kudin fansa naira miliyan 10 sannan suka kashe shi daga baya. Wannan kadan ne daga cikin abubuwan da muke ciki.”

Bangaren yan sanda

A halin da ake ciki, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Borno

A wani labari na daban, sojojin Najeriya sun yi gagarumin nasara inda suka kai samame kan yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.

Kara karanta wannan

An Kona Gidan Jigon PDP Awa 24 Bayan Gwamna Ya Masa Kyautar Sabuwar Mota A Babban Jihar Arewa

Jirgin yakin NAF ya sauke bama-bamai guda bakwai a kan mayakan kungiyar ta'addancin yayin da suke zirga-zirga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel