Dakarun Sojoji Sun Yi Nasarar Bindige Yan Fashi 4 a Jihar Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Yi Nasarar Bindige Yan Fashi 4 a Jihar Kaduna

  • Sojoji sun yi gagarumin nasara a kan yan bindige inda suka bindige mayaka hudu a yankin Chikun da ke jihar Kaduna
  • Dakarun Operation Forest Sanity sun cimma wannan nasara ne a wani farmaki da suka kai mabuyar yan fashin
  • Da take tabbatar da lamarin, gwamnatin Kaduna ta ce jami'an tsaron sun kwato makamai da babur

Kaduna - Dakarun Operation Forest Sanity sun kashe yan fashi da makami hudu yayin wani samame da suka kao mabuyar miyagun a kauyen Tsohon Gayan da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba, Channels TV ta rahoto.

Jihar Kaduna
Dakarun Sojoji Sun Yi Nasarar Bindige Yan Fashi 4 a Jihar Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda sojojin suka aiwatar da kisan

Ya bayyana cewa dakarun sun fatattaki yan bindigar da ke tserewa kuma a cikin haka ne suka kashe biyu daga cikinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyoyi na sirri sun kuma bayyana cewa wasu biyu sun mutu sakamakon raunukan da suka ji ta sanadiyar harbin bindiga, rahoton Vanguard.

A cewar kwamishinan, majiyoyi abun dogaro a yankin gaba daya sun rahoto cewa sunayen biyu daga cikin yan bindiga hudu da aka kashe sune Dogo Mallam da Bello Mallam.

Dakarun sun kuma samo wata bindigar AK47 daya, harsashen 22 da babur daya.

Sojoji sun bindige yan Boko Haram 5, sun kuma danke daya

A wani labarin kuma, dakarun rundunar sojoji da ke yaki da masu tayar da kayar baya a yankin arewa maso gabas na ci gaba da namijin kokari don ganin sun kawo karshen yan ta'addan da suka addabi yankin.

A cikin haka ne, sojojin Operation Hadin kai suka sheke mayakan Boko Haram biyar lahira sannan suka cika hannu da wani dan ta'adda guda a jihar Borno.

Sojojin sun yi wannan nasara ne a ranar Alhamis da ya gabata bayan sun yi aiki kan bayanan sirri da ke tabbatar da shige da ficen mayakan kungiyar ta'addancin a yankin Mafa da ke jihar.

An mika dan ta'adda guda da ya shiga hannu ga rundunar sojojin kasar domin gudanar da bincike yayin da dakarun suka zafafa yin faturol a yankin don yakar sauran yan ta'adda a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel