Da Duminsa: Lakcarori Zasu Sha Jar Miya, FG Ta Basu Albashin Rabin Wata

Da Duminsa: Lakcarori Zasu Sha Jar Miya, FG Ta Basu Albashin Rabin Wata

  • Gwamnatin tarayya ta gwangwaje malamai masu koyarwa na jami’o’in Najeriya Albashin rabin watan Oktoba da yammacin ranar Alhamis
  • Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, an biya rabin albashin watan Oktoban ne bayan kwanaki 18 da suka janye yajin aikin da suka yi wata 8 suna yi
  • Idan za a tuna, malaman sun koma bakin aikinsu tun ranar 14 ga watan Oktoba, bayan watanni takwas da suka kwashe suna zaman gida

Gwamnatin tarayya ta biya lakcarorin jami’a dake karkashin kungiyar malamai masu koyarwa ta ASUU albashin kwanaki 18 na watan Oktoba, Legit.ng Hausa ta tabbatar da hakan.

Lakcarori da dama da Legit.ng Hausa ta tuntuba sun tabbatar mata da hakan inda suka ce an biya su rabin albashinsu ne kuma yana nuna na watan Oktoba.

An rahoto yadda malaman jami’an suka koma yajin aikin watanni takwas da suka yi a ranar 14 ga watan Oktoban 2022. An yi kira ga lakcarorin da su koma bakin aiki a ranar da aka janye yajin aikin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kamfanin Jirgin Emirates Na Dubai Ya Daina Jigilar Fasinjoji Zuwa da Fita Daga Najeriya

A bayanin da wani malamin jami’a yayi wa Legit.ng Hausa, yace ya samu albashin babu zato balle tsammani duk da cewa ba wannan bace yarjejeniyar dake tsakaninsu da gwamnatin tarayya ba.

”Na samu Albashin wurin karfe shida na yammacin Alhamis, 3 ga watan Nuwamban 2022. Rabonmu da jin shigowar albashi tun a wata Fabrairu.
”Ba zan ce ina daukin kudin ba saboda tuni na gane cewa ba zan iya rayuwa a kan albashina ba. Shiyasa na kama wasu ayyukan tun kafin ma a tafi yajin aiki.“

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Malamin jami’an da ya bukaci a boye sunansa ya sanar.

Ita kuwa Malama Fatima Bello, tace ta matukar jin dadin shigowar wannan Albashin tunda dama iya wahala sun dandana.

”Daga ni har mijina malaman jami’a ne, idan nace wannan watannin da muka kwashe babu albashi nayi su cikin walwala, gaskiya nayi karya.

Kara karanta wannan

Mummunar Gobara Ta Yi Ajalin Bayin Allah Sama da 10 a Kano

”Amma kuma wannan zan iya cewa ya zama darasi gareni da ire-irena da suka riki koyarwa a jami’a matsayin aikin yi daya tak.
”Yanzu ina fatan su kammala biyanmu in tada jari mai tsoka saboda halin ko ta kwana.”

- Lakcarar mai ‘ya’ya biyu tace.

Babban Abin da Ya sa Muka Hakura, Muka bude Jami’o’i Bayan Wata 8 inji ASUU

A wani labari na daban, Shugaban kungiyar ASUU ta malaman jami’a, Emmanuel Osodeke yace hukuncin kotu ne babban abin da ya tursasa masu komawa bakin aiki.

The Cable ta rahoto Farfesa Emmanuel Osodeke yana mai cewa malamai sun janye yajin-aikin da su ke yi ne saboda Alkali ya umarci su bude makarantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel