Dalilan da Suka Jawo Buhari Ya Fatattaki Shugaban NYSC Daga Yin Wata 6 a Ofis

Dalilan da Suka Jawo Buhari Ya Fatattaki Shugaban NYSC Daga Yin Wata 6 a Ofis

  • Birgediya Janar Muhammad Fadah bai dade a kan kujerar NYSC ba, shugaban kasa ya sallame shi
  • Bayan Manjo Janar Ibrahim Shuaibu ya bar hukumar ne sai aka nada Brig Gen MK Fadah a watan Mayu
  • Ana jifan NYSC DG da badakalar satifiket, shekaru, rashin sanin aiki, da nuna son kai wajen aikinsa

Abuja - Bayanai sun fito game da abin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke Muhammad Fadah daga kujerar shugaban hukumar NYSC.

Birgediya Janar Muhammad Fadah bai wuce watanni shida yana rike da hukumar kula da harkar bautan kasa ba, Shugaban Najeriya ya yi waje da shi.

Bayanan da Premium Times ta samu ya nuna cewa an zargi Janar Muhammad Fadah da laifuffukan nuna son kai da rashin gaskiya wajen aikinsa.

Haka ana tuhumar Sojan da nuna bambancin addini a yadda ya tafiyar NYSC.

Kara karanta wannan

Atiku: Zan Fitar Da Sunayen Ɓarayin Man Fetur, Zan Kunyata Su Idan An Zabe Ni Shugaban Ƙasa A 2023

An aika da korafi ga Minista

Shugabar majalisar da ke sa ido a kan aikin NYSC a Najeriya, Fatima Abubakar ta aika takarda zuwa ga Ministan wasanni da matasa a kan Darektan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun farko majalisa tana zargin cewa akwai alamar tambaya a kan shaidar karatun Birgediya Janar Muhammad Fadah da shekarunsa a doron Duniya.

'Yan NYSC
Ana rantsar da 'Yan NYSC Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Fadah bai wanke kan shi ba

Kamar yadda wannan kebantaccen rahoto ya nuna, an bukaci Fadah ya wanke kan sa daga wannan zargi, amma ya gagara yin hakan, har aka sauke shi.

A wasikar da aka aikawa Sunday Dare, an ankarar da shi cewa sabon Darekta Janar din bai dauki aikinsa da gaske ba, kuma da alamun bai da kwarewa.

Sannan an jefi Janar Farah da rashin basira, wanda hakan bai dace ga wanda zai jagoranci ragamar matasan da za su zama manyan gobe a Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Shin da gaske EFCC ta kame dan Peter Obi bisa laifin damfara? Gaskiyar magana ta fito

Korafe-korafe akalla uku da ake da su a kan Darekta Janar din sun shiga hannun jama’a, don haka majalisar take ganin wannan zai iya bata mata suna.

Babu jituwa da Sunday Dare

A gefe guda, Ministan tarayya ya saurari korafin da aka gabatar, don haka ya rubutawa shugaban kasa takarda cewa ayi tunbuke shugaban na NYSC.

Rahoton yace duk da zargin da ake yi masa, an tuhumi Farah da rashin biyayya ga Minista da rashin bin doka, yana ganin tsawon kafansa ya kai shi ofis.

Babu kudin kula da jiragen sa

Kuna da labari Najeriya ta na amfani da jiragen saman Boeing Business Jet (Boeing 737-800/NAF 001), Gulfstream G550, da su Gulfstream V (Gulfstream 500.

Sai dai ana fuskantar matsaloli domin gwamnatin tarayya tana fama da karancin kudin kula da jiragen da saya masu kayan aikin da ake bukata wajen tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel