Kotu Ta Tsige Dukkan Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi Da Kansiloli A Shahararriyar Jihar Kudu

Kotu Ta Tsige Dukkan Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi Da Kansiloli A Shahararriyar Jihar Kudu

  • Kotun tarayya da ke Osogbo ta kori dukkan ciyamomi da kansiloli da ake zaba a baya-bayan nan a jihar Osun
  • Kotun ta ce an saba doka wurin fitar da sanarwar fara zaben hakan yasa sakamakon zaben ba zai yi tasiri ba
  • A bangarenta, jam'iyyar APC ta jihar Osun ta bakin kakakinta ta ce za ta daukaka kara, ta shawarci mambobinta su kwantar da hankulansu

Osogbo, Jihar Osun - Babban kotun tarayya da ke zamanta a Osogbo, a jihar Osun, a ranar Juma'a ta kori dukkan sabbin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Mai shari'a Nathaniel Emmanuel-Ayoola ya ce zaben da Hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Osun, OSIEC, ta yi ya saba da sashi na 29 da 32 da dokar zabe na shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Atiku: Zan Fitar Da Sunayen Ɓarayin Man Fetur, Zan Kunyata Su Idan An Zabe Ni Shugaban Ƙasa A 2023

Kotun
Kotu Ta Tsige Dukkan Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi Da Kansiloli A Osun. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An saba doka yayin sanar da yin zabe - kotu

Wanda ya shigar da kara, jam'iyyar PDP, ta yi ikirarin cewa, sanarwar zaben da aka fitar a 15 ga watan Agustan 2022, ya saba wa doka kuma ta roki kotun ta ayyana zaben a matsayin wanda ya ci karo da doka, kuma babu shi.

Kamar yaddda The Sun ta rahoto, kotun ta ce sanar da zaben na da matukar muhimmanci, kuma sashi na 150(3) na dokar zabe ya ce duk wani zaben da aka gudanar ba bisa doka ba ba zai yi tasiri ba.

Mai shari'a Ayoola ya ce an fitar da sanarwar zaben ne a ranar 15 ga watan Agustan 2022, kuma an yi zaben a ranar 15 ga watan Oktoban, hakan na nusa notis din kwana 60 aka bayar, yana mai cewa hakan ya saba doka don haka zaben ba bisa ka'ida aka yi shi ba kuma ba zai yi tasiri ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu, Atiku, Obi, Da Wasu Suna Cikin Matsala Yayin Da INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka'idoji

Za mu daukaka kara - jam'iyyar APC ta Osun

Mai magana da yawun jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Kola Olabisi ya ce jam'iyyarsa za ta daukaka kara kuma ya shawarci mambobin jam'iyyar su kwantar da hankulansu.

Kotu ta soke zaben cikin gida na APC a jihar Ribas

Babban kotu da ke zamanta a Fatawal ta soke zaben cikin gida da jam'iyyar APC ta yi a jihar Ribas, The Sun ta rahoto.

A cewar rahoton Vanguard, kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin bayan sauraron kara da wasu fasatattun yan APC suka shigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel