Da Duminsa: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani Na APC a Wata Jiha, Ta Yi Fatali da Wadanda Suka Ci Zabe

Da Duminsa: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani Na APC a Wata Jiha, Ta Yi Fatali da Wadanda Suka Ci Zabe

  • Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta hadu da babban cikas a jihar Ribas gabannin babban zaben 2023
  • Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Port Harcourt ta soke zaben fidda gwanin da jam’iyyar tayi a jihar
  • Mai shari’a E.A. Obile ne ya zartar da hukunci a wata kara da wasu fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar suka shigar gabansa

Rivers - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Port Harcourt ta soke zaben fidda gwanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas, rahoton The Sun.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kotun ta zartar da hukuncin ne a jiya Litinin yayin sauraron wata kara da wasu fusatattun mambobin APCn suka shigar a gabanta.

Tambarin APC
Da Duminsa: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani Na APC a Wata, Ta Yi Fatali da Wadanda Suka Ci Zabe Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: UGC

Idan za a tuna, fusatattun mambobin sun yi zargin cewa an ware su a yayin zaben fidda gwanin jam’iyyar inda suka yi zanga-zanga sakatariyarta da ke Port Harcourt.

Kara karanta wannan

Shaidanun APC Sun Dade Da Komawa PDP, In ji Tsohon Minista

Sai dai kuma, wani mai suna George Orlu da wasu mutane hudu da suka yi ikirarin siyan fam din takara sun tunkari kotu inda suka bukaci a soke zaben fidda gwanin APC a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take yanke hukunci, kotun ta bayyana cewa an tsame mutanen daga zaben fidda gwanin ba bisa ka’ida ba.

Justis E.A. Obile, a hukuncinsa, ya riki cewa an fitar da fusatattun mutanen daga zaben fidda gwanin ba bisa doka ba, yana mai cewa hakan yasa aka soke shi.

Obile ya yarda da masu karar cewa an tsame su a tsarin shiga zaben fidda gwanin jam’iyyar ba bisa ka’ida ba.

Don haka ya yanke hukunci cewa an soke zaben kuma kada a dauki wadanda aka zaba a tsarin a matsayin yan takara.

Kotu Ta Ayyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC Na Wata Jiha a 2023

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Ayyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC Na Wata Jiha a 2023

A wani labarin kuma, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Calabar ta ayyana Bassey Otu a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Cross River.

Justis Ijeoma Ojukwu ce ta ayyana haka yayin da take zartar da hukunci a kan wata kara da aka shigar a gabanta, Channels TV ta rahoto.

Bayan zaben fidda gwanin APC a watan Mayu, Owan Enoh wanda yana daya daga cikin wadanda suka nemi takarar tikitin gwamna na jam’iyyar mai mulki a jihar ya garzaya kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel