Adadin Talakawan Dake Kano, Kaduna, Katsina, Da Sauran Jihohin Arewa Maso Yamma

Adadin Talakawan Dake Kano, Kaduna, Katsina, Da Sauran Jihohin Arewa Maso Yamma

  • Majalisar dinkin duniya UN ta yi ta'arifin talaka a matsayin wanda bai iya samun alal akalli $2 a rana.
  • A yau ana samun Dalar Amurka $1 kudi N443.45 a banki; Amma N780 a kasuwar bayan fagge
  • Hakan na nufin cewa duk wanda ai samun akalla N1500 a rana Talaka ne. Wannan na nufin abincin safe N500, na rana N500, na dare N500

Gwamnatin tarayya da hukumar kididdigar kasa NBS ta saki rahoton adadin mutanen dake cikin bakin talauci a kasar a shekarar 2022.

NBS a sabon rahoton da ta fitar ranar 17 ga Nuwamba.

Ta bayyana cewa kashi 63 na dukkan ‘yan Najeriya suna cikin matsanancin talauci tare da fatara.

Hakan na nufin mutum miliyan 133 ne ke cikin bakin talauci na rashin abinci, kiwon lafiya, aikinyi, ilimi, dss.

Kara karanta wannan

Jerin Talakawan Dake jihohin Gombe, Yobe, Taraba, Bauchi, Borno, Adamawa: NBS

A fadin Najeriya gaba daya, Jihar Sokoto ce tafi yawan Talakawa, bisa jadawalin TheCableIndex.

Gwamnatin Buhari dai a bayan ta yi alkawarin fitar da yan Najeriya milyan 100 daga cikin kangin talauci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje
Adadin Talakawan Dake Kano, Kaduna, Katsina, Da Sauran Jihohin Arewa Maso Yamma
Asali: UGC

Ga jerin adadin mutanen da cikin talauci a jihohin Arewa maso gabas:

JihaAdadin Talakawa%
SokotoMutum Milyan 5.890.5%
JigawaMutum Milyan 5.884.3%
KebbiMutum Milyan 4.382.2%
ZamfaraMutum Milyan 4.278%
KadunaMutum Milyan 873.9%
KatsinaMutum Milyan 6.972.7%
KanoMutum Milyan 10.566.3%

Sharhi

Bisa jadawalin, mutum kashi 9.5% na al'ummar jihar Sokoto ne kadai suke ci su koshi lafiya kulli yaumin.

Jihar Jigawa da Kebbikuwa, kashi 15% kacal ke samun cin abincin N500 da safe, N500 da rana, kuma N500 da dare.

A jihar Kaduna da Zamfara, kashi 26% dan dauri ne masu walwala.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Zakulo Mutane 30, Ya Naɗa Su Manyan Mukamai a Gwamnatinsa

Yan jihar Kano ne kadai suke da masu walwala da ya haura kashi 30%. Duk da haka, mutum biyu cikin ukun yan jihar Kano basu ci su koshi yadda ya kamata a rana.

Wannan Alkaluma na nuna cewa mafi akasarin al'ummar yankin Arewa maso yamma Talakawa ne.

Wadanda talauci yafi afkawa sune masu iyalai da yawa saboda zasu ji da kudin abinci, kudin muhalli, kudin makaranta da kudin kiwon lafiyan iyali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel