Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Zubar Da Hawaye Yayin Da Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Karshe A Matsayin Gwamna

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Zubar Da Hawaye Yayin Da Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Karshe A Matsayin Gwamna

  • Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 na jiharsa gaban majalisar dokoki
  • Yayin gabatarwar kasafinsa na karshe a matsayin gwamna wanda wa'adinsa na biyu ta kusa karewa, Masari ya zubar da hawaye saboda halin da ya tsinci kansa a lokacin
  • Masari ya ce gwamnatinsa ta cika wa mutane jihar mafi yawancin alkawurra da ta dauka a bangaren ilimi, muhalli, albarkatun ruwa, kiwon lafiya, muhallli dss

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya gabatar da kasafin kudi na Naira biliyan 288.63 na shekarar 2023, Daily Trust ta rahoto.

Yayin da ya ke gabatar da kasafin a gaban majalisar dokokin jihar Katsina a ranar Talata, gwamnan ya shiga wani yanayi har ya gaza rike hawayensa duba da cewa wannan ne karo na karshe da zai gabatar da kasafi gaban majalisar don wa'adinsa ta kusa karewa.

Kara karanta wannan

Komai Ya Yi Farko: Gwamnan Arewa Ya Zubar Da Hawaye Yayin Gabatar da Kasafin Kudi Na Karshe

Masari
Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Zubar Da Hawaye Yayin Da Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Karshe A Matsayin Gwamna. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi wa'adi biyu a ofis.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Kamar yadda kuka sani, wannan shine karo na karshe da zan tsaya gaban mambobin majalisar dokokin jihar Katsina don gabatar da kasafin shekara na jihar Katsina.
"An tsara kasafin ne don karfafa nasarorin da muka samu a matsayin gwamnatin jihar Katsina cikin shekaru bakwai da rabi da suka gabata."

Jimilar kasafin kudin shekarar ta 2023 ya kai N288,633,257,963.00 tare da kashi 63.77% na jari da kuma kashi 36.23% na kudaden kashewa akai-akai, The Guardian ta rahoto.

Gwamnan ya ce:

"A dunkule, kasafin kudin na 2023 bai kai kasafin 2022 ba da aka yi wa kwaskwarima da N34,662,962,998.00. Kasafin kudin 2023 an tsara shi ne da jimillar kashe kudade akai-akai na N104,580,485,996.28 wanda ya yi daidai da kashi 36.23% na kasafin kudi da kudin kashewa na N184,052,771,966.72 wanda ya kai kashi 63.77% na jimillar kasafin kudin."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

A cewar gwamnan, kasafin kudin shekarar 2023 mai lakabin “Budget of Transition” an tsara shi ne domin kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma kaddamar da wasu manyan ayyuka da za a iya kammala su kafin wa'adinsa ya kare.

Kason da muhimman bangarori suka samu a kasafin

Muhalli ya sami kaso mafi girma na 17.25 cikin dari, sannan albarkatun ruwa a kashi 15.87 da lafiya a kashi 13.03 cikin dari. Sauran su ne ayyuka, kashi 11.41 cikin dari; ilimi, kashi 10.12 cikin dari da ayyukan gona a kashi 7.39 cikin dari yayin da sauran MDAs suka samu kashi 24.93 cikin dari.

Gwamna Masari ya ce gwamnatinsa ta cika galibin alkawurran da ta dauka yayin kamfen kan ilimi; kiwon lafiya; albarkatun ruwa; muhalli da tituna da gine-gine na cigaba karkashin 'restoration agenda'.

Jawabin kakakin majalisar Katsina

A jawabinsa, kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Tasiu Musa Maigari, ya bawa gwamnatin tabbacin majalisar ba za ta bata lokaci ba wurin nazari kan kasafin da ya gabatar don biyan bukatun mutanen jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Tsinci Kansa A Matsala Kan Sukar Peter Obi, Matasan Ibo Sun Bayyana Matakin Da Za Su Ɗauka A Kansa

Ya ce:

"Saboda haka, ina kira ga ma'aikatu, sassan gwamnati da hukumomi da su bayyana a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai domin kare kiyasin da suka yi kuma su kiyayye jadawalin kare kasafin kudin da za a aika musu nan bada dadewa ba."

Ku Yafe Mun Kura-Kuran da Na Tafka a Zamanin Mulkina, Masari Ya Roki Katsinawa

A wani rahoton, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya roki mazauna jihar su yafe masa duk wani kuskure da ya yi a zamanin mulkinsa na tsawon zango biyu dake gab da karewa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Gwamna Masari ya nemi wannan afuwar ne a wurin taron ƙaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen jam'iyyar APC a jihar yau Litinin 31 ga watan Oktoba, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel