Uwargida Ta Siyawa Mai Gida Mota Kirar Ferraru, Martaninsa Ya Ba Jama’a Mamaki

Uwargida Ta Siyawa Mai Gida Mota Kirar Ferraru, Martaninsa Ya Ba Jama’a Mamaki

  • Wata mata ta nuna kauna da don mijinta ya ji dadi yayin da ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta wani salo mai ban mamaki
  • A wani bidiyon da aka yada a TikTok, an ga lokacin da matar ke damkawa mijinta mota kirar Ferrari, lamarin da ya jawo cece-kuce
  • Martanin da mijin ya yi ba yawo rabuwar kai a TikTok, wasu sun bayyana ra'ayinsu kan yadda mijin ya amshi kyautar

An yi ta cece-kuce yayin da wani bidiyo ya nuna yadda mata ta ba mijinta kyautar mota kirar Ferrari.

A bidiyon da Pweedy Mum Boiz ya yada a TikTok, an ga lokacin da matar ta dauki zagayowar ranar haihuwar mijinta da muhimmanci, ta kuma taya shi murna.

An yada bidiyon ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, kuma ya nuna yadda aka zo da mijin idonsa a rufe, sai kuma aka bude idonsa ya ga abin mamaki.

Kara karanta wannan

Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

Abokai da masu fatan alheri sun taru don shaida wannan rana, ga kuma mai busa algaita a gefe na yi don kara wa bikin armashi.

Mata ta ba da mamaki yayin da ta gwangwaje mijinta da kyautar mota
Uwargida Ta Siyawa Mai Gida Mota Kirar Ferraru, Martaninsa Ya Ba Jama’a Mamaki | Hoto: TikTok/@pweedymumboiz.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma dai mijin bai iya soyayya ba

Sai dai, wasu 'yan TikTok sun nuna damuwa kan abin da mijin ya yi a gaban jama'a duk da basu babbar kyauta irin wannan.

A cewarsu, ya ki ya nuna farin ciki duk da kuwa ya ga an bashi galleliyar mota. Don haka suka ce bai iya soyayya ba.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

@user8938827520189 yace:

"Wow abin sha'awa, a kasa ta muna yiwa maza ba zata ne da gwajin juna biyu."

@Ka-dee tace:

"Aiki mai yawwa amma babu wadataccen nuna jin dadi."

@pat Ben yace:

"Amma dai wannan mutumin bai iya soyayya soyayya ba ko kadan. Haka kawai ya bata min rai"

Kara karanta wannan

Hoton ‘dan Najeriya Ya Kai $500k Banki Domin Adanawa ya Ba Jama’a Mamaki

@great.nicole2017 yace:

"Kawai ya tuna kudadensa da aka sace ne a dakin kwana, lol."

@Kamp2Sene yace:

"Ina da ta cewa da yawa, amma babu ruwa na."

@P.I. yace:

"Ita kadai ne take nuna annashuwa...zuciyarta ne. Kyakkyawar mata ce. Allah yasa kada ta taba ganin wata mace tare da shi a Ferrarin."

Ba wannan ne karon farko da mata ke yiwa maza kyautar mota ba, an sha samun irin wadannan lokuta masu ban annashuwa a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel