Kotu Ta Garƙame Fulani Makiyaya Uku Sakamakon Kone Gonar Gyada Ta Miliyan N1.5m

Kotu Ta Garƙame Fulani Makiyaya Uku Sakamakon Kone Gonar Gyada Ta Miliyan N1.5m

  • Kotu ta ba da umarnin a tsare wasu makiyaya a gidan Gyaran hali bisa zargin kona gonar Gyaɗa da ta kai miliyan N1.5m
  • A zaman Kotun, waɗanda ake zargin sun ce sun aikata haka ne domin rama abinda mai gonar ya musu a bara
  • Bayan sauraron kowane ɓangare, Alkalin Kotun ya sanar ɗage zaman zuwa rana ta gaba

Kebbi - Kotun Majistire dake zama a jihar Kebbi ranar Talata ta umarci a tasa ƙeyar wasu Makiyaya uku zuwa gidan gyaran hali bisa zargin ƙone Gonar Gyaɗa.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Gonar da ake zargin makiyayan sun ƙone ta kai darajar kuɗi Naira miliyan Ɗaya da rabi.

Fulani Makiyaya.
Kotu Ta Garƙame Fulani Makiyaya Uku Sakamakon Kone Gonar Gyada Ta Miliyan N1.5m Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Waɗanda ake zargin da suka haɗa da, Riskuwa Mode, Manu Kinasa da kuma Sanda Kiruwa, an ce sun cinna wa Gonar wuta da gangan a ƙauyen Mashekari Geza, ƙaramar hukumar Bunza a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

2023: Kotun Daukaka Kara Ta Kwace Tikitin Ɗan Takarar PDP a Kano, Ta Baiwa Mace

Alkalin Kotun mai shari'a Hassan Muhammad Kwaido, ya nemi jin maƙasudin ƙone Gonar daga bakin waɗanda ake zargi kuma a bayanansu sun ce abinda suka yi ramuwar gayya ce kan abinda mai gonar ya aikata musu bara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsu,

"Bayan sun bar Shanunsu sun shiga Gonarsa sun cinye amfanin da ya shuka, Sai ya kama musu Dabbobi kuma aka tilasta musu biyan ɓarnar, dole suka sayar da Dabba ɗaya sannan suka iya biya."

Sakamakon wannan abu da ya musu a shekarar da ta gabata ne suka cinna wa Gonarsa wuta da gangan, inji waɗanda ake zargi.

Wane mataki Kotun ta ɗauka kansu?

Lauyan waɗanda ake ƙara, Y. A Aminu, ya yi nasarar karɓan Belin mutum biyu daga cikinsu yayin da ɗayan aka tasa ƙeyarsa zuwa Gidan Gyaran Hali saboda ya amsa cewa shi ne ya cinna wutar da hannunsa.

Kara karanta wannan

Na Ɗirka Wa Budurwata Ciki da Izinin Mahaifiyarta, Matashi Sadiq Ya Yi Wa Kotu Bayani Dalla-Dalla

Bayan haka ne Alƙalin Kotun ya ɗage zaman zuwa rana ta gaba domin dawowa a ci gaba da sauraron shari'ar.

Wani manomi a garin Dabai, jihat Katsina ya shaida wa wakilin Legit.ng cewa ɓarnar da Fulani ke wa manoma a wannan shekarar ta wuce yadda ake tsammani.

Saifullahi Lawan, wanda aka je har gona aka kwashe Shinkafar da ya noma, yace da mahukunta zasu rika ɗaukar mataki irin haka watakila da an samu sauki.

Yace:

"Naji daɗin matakin Kotu domin barnar da Makiyaya ƙara yawa take, baki ɗaya aka kwashe mun Shinkafa a gonata. Ban kai ƙara ba ko waye na barsu da Allah."
"Maganar gaskiya abubuwan dake zuwa daga baya irinsu dawa, ɗa msu shuka Wake bayan girbi da Tumatir dole suke ɗaukar mataki sbaoda kwararar makiyaya, abin ya yi wa Allah ya kawo mana karshensa.

Haka zalika, Umar Idris, mazaunin garin Ɗanja a Katsina yace dole ta sa ya kwaso Wakensa da wanda ya nuna da wanda bai nuna ba saboda gudun asara.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Matafiya 17 da Suka Taso Daga Gombe Sun Gamu Da Ajali, Sun Kone Kurmus

"Abun takaicin ka gama kashe kuɗin noma duk da yadda rayuwa ta yi tsada amma mutanen nan su zo da shanu rana ɗaya su takaitaka kuma ba yadda muka iya," inji shi.

A wani labarin kuma A cigaba da shari'ar Kisan Ummita, Ɗan sanda mai bincike ya ba da shaida a zaman babbar Kotun jihar Kano

Masu shigar da ƙara ƙarƙashin kwamishinan shari'a na jihar Kano, Barista Musa Lawal Abdullahi sun gabatar Insifekta Injuptil Mbambua a matsayin shaida ta 5.

Da yake faɗin binciken da suka gudanar, ɗan sandan yace Ɗan China da ake zargi ya kashe wa Marigayya Ummita makudan kuɗaɗe bayan ta masa alƙawarin aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel