Na Dirka Wa Budurwata Ciki Ne Da Izinin Mahaifiyarta, Wani Matashi Sadiq Ya Faɗa Wa Kotu

Na Dirka Wa Budurwata Ciki Ne Da Izinin Mahaifiyarta, Wani Matashi Sadiq Ya Faɗa Wa Kotu

  • Wani matashin saurayi mai suna Sadiq ya gaya wa Alkalin Kotu a Ibadan cewa Surukarsa ce ta bukaci ya yi wa ɗiyarta ciki
  • A jawabin kare kansa a zaman Kotu, Matashin yace ya yi mamakin yadda iyayen budurwar suka juya masa baya tun kafin aure
  • Kotun ta yanke hukuncin miƙa kula da yaron hannun budurwar kana ta umarci Sadiq ya rika ba ta dubu N10,000 duk wata

Ibadan, Oyo - Wani matashi mai suna Sadiq ya faɗa wa wata Kotu a Ibadan babban birnin jihar Oyo, cewa mahaifiyar budurwarsa ce ta nemi ya ɗirka wa ɗiyarta ciki kafin a ɗaura musu aure.

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa Sadiq ya bayyana wa Kotu komai ne yayin da yake kokarin kare kansa a zaman Shari'ar da budurwar ta kai shi ƙara.

Kara karanta wannan

'Ramuwar Gayya Muka Yi': Kotu Ta Yanke Wa Wasu Makiyaya Uku Hukunci Kan Ƙone Gonar Gyaɗa Ta Miliyan N1.5m

Matsalolin soyayya.
Na Dirka Wa Budurwata Ciki Ne Da Izinin Mahaifiyarta, Wani Matashi Sadiq Ya Faɗa Wa Kotu Hoto: aminiya
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa budurwar, wacce ta riga ta haife cikin, ta kai ƙarar Sadiq ne bisa zargin baya bata kulawar da ya kamata.

Da yake wa Alƙali jawabi a zaman Kotun, wanda ake zargi yace ya aikata abinda iyayen budurwarsa suka nema a wurinsa amma daga baya kuma suka juya masa baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Ban san wace matsala ce ta faru ba, iyayen yarinyar suka same ni suka gaya mun cewa sam ba zasu amince ɗiyarsu ta zauna zaman aure da ni ba. Kuma an hana ni ganin ɗan da ta haifa mun."

Tun da farko mai shigar ƙara ta gaya wa Alkalin Kotun cewa Saurayin ya watsar da ita, ba ya bata kulawa da ɗanta da suka haifa mai shekara uku.

Tace:

"Tunda Allah ya sauke ni lafiya ina ga sau biyu kacal ya bani kuɗi N1,500 da kuma kayan jariri. Daga nan kuma ya daina sauke nauyin dake wuyansa."

Kara karanta wannan

'Yan Daba Sun Kai Farmaki Wurin Gangamin Yakin Neman Zaben Atiku a Gombe, Sun Yi Ɓarna

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Alkalin Kotun mai shari'a Misis S.M. Akintayo tace babu wani aure da za'a raba tsakanin mutanen biyu domin a iya abinda ta fahimta ba'a kai ga ɗaura aurenba tunda babu Sadaki.

Ta kuma yanke hukuncin cewa yaron ya zauna a wurin mahaifiyarsa yayin da shi kuma Sadiq zai rinƙa baiwa budurwar N10,000 a kowane wata.

A wani labarin kuma Miji Ya Fadi Yadda Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa da Dan Uwansa, Ya Nemi Saki a Kotu

Justice Oni, wani ɗan kasuwa a Abuja ya nemi Kotu ta raba aurensa da mai ɗakinsa saboda ta cika neman maza tana neman sa masa hawan jini.

Da yake labarta wa Kotu abubuwan da idonsa sjka gani, yace ya ga matarsa ta na lalata da ɗan uwansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel