Tashin Hankali: Mutane 37 Sun Mutu Yayin Da Motocin Bas Suka Yi Karo Da Juna a Borno

Tashin Hankali: Mutane 37 Sun Mutu Yayin Da Motocin Bas Suka Yi Karo Da Juna a Borno

  • Kimanin mutane 37 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a karamar hukumar Kondugua a Borno
  • Hatsarin ya faru ne a lokacin da wasu motoccin bas guda biyu masu daukan mutane 18 suka yi karo da juna misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata 22 ga watan Nuwamba
  • Hukumar kiyayye haddura na kasa FRSC reshn jihar Borno ta tabbatar da afkuwar hatsarin ta bakin kwamandanta mai suna Utten Iki Boyi inda ya ce abin bakin ciki ne

Borno - A kalla mutane 37 ne suka rasu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota tsakanin bas biyu masu daukan mutum 18 a babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a karamar hukumar Kondugua na jihar Borno.

Kara karanta wannan

Mutum 23 Sun Yanke jiki sun Fadi Yayin Tattakin Goyon Baya ga Tinubu da Shettima a Kano

Daily Trust ta tattaro cewa hatsarin ya faru ne misalin karfe 10 na safiyar yau Talata 22 ga watan Nuwamban shekarar 2022.

Taswirar Borno
Tashin Hankali: Mutane 37 Sun Mutu Yayin Da Motocin Bas Suka Yi Karo Da Juna a Borno. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Hukumar FRSC ta tabbatar da afkuwar hatsarin

Kwamanda na hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC a jihar Borno, Utten Iki Boyi, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga majiyar Legit.ng, yana mai cewa ya kirga gawarwarki 37 baya ga wadanda suka kone.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"A halin yanzu da muke gana, hankali ne ba a kwance ya ke ba."

Boyi ya kara da cewa:

"Mun rasa mutane biyar a hatsarin mota a wannan babban hanyar a jiya, abin bakin ciki ne."

Hakan na zuwa ne awanni bayan wasu fasinjoji da ke kan hanyarsu zuwa Legas daga Gombe sun kone sakamakon hatsarin mota.

PM News ta rahoto Boyi na cewa mutanensa da yan sanda da jami'an NEMA da yan kwana-kwana suna taru suka kwashe wadanda abin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun kassara karfin Turji, sun yi kaca-kaca da maboyar mai kawo masa makamai

A cewarsa, yan sanda sun samu umurni daga kotu na yi wa wadanda suka rasu jana'iza.

NAN ta rahoto cewa wani hatsari ya faru a wannan titin a ranar Litinin da ya ritsa da wani bas mai dauke da fasinjoji 10 inda biyar suka rasu.

Fitaccen Dan Siyasan Arewa Ya Mutu A Hatsarin Mota

Kwamishinan Matasa Da Wasanni na Jihar Yobe, Honarabul Goni Bukar Lawan, (BUGON) ya mutu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Kano.

Goni Bukar, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda aka fi sani da BUGOM, ya rasu a daren yau Talata a hanyarsa na zuwa Jihar Kano, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel