Yanzu-Yanzu: Fitaccen Dan Siyasan Arewa Ya Mutu A Hatsarin Mota

Yanzu-Yanzu: Fitaccen Dan Siyasan Arewa Ya Mutu A Hatsarin Mota

  • Allah ya yi wa kwamishinan matasa da wasanni na Jihar Yobe, Honarabul Goni Bukar Lawan wanda aka fi sani da BUGON rasuwa
  • Tsohon dan majalisar tarayyar ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da shi a hanyar Damaturu zuwa Kano a daren ranar Talata 2 ga watan Agusta
  • Rahotanni sun bayyana cewa mamacin ya hallarci wata jana'iza ne a garin Damaturu a ranar Talatar amma shima Allah ya masa rasuwa a hanyarsa na tafiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Yobe - Kwamishinan Matasa Da Wasanni na Jihar Yobe, Hon. Goni Bukar Lawan, (BUGON) ya mutu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Kano.

Goni Bukar, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda aka fi sani da BUGOM, ya rasu a daren yau Talata a hanyarsa na zuwa Jihar Kano, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Tsohon Shugaban Jami'ar LASU, Farfesa Hussein, Ya Rasu

Jihar Yobe.
Fitaccen Dan Siyasan Arewa Ya Mutu A Hatsarin Mota. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta ambaci majiya na cewa mamacin ya hallarci jana'iza a Damaturu babban birnin Jihar Yobe a yammacin ranar Talata, kafin ya kama hanyar zuwa Jihar Kano.

Za a yi jana'izarsa a ranar Laraba a Damaturu domin an koma da gawarsa Damaturu babban birnin jihar Yobe a daren ranar Talata, Daily Indepedent ita ma ta rahoto.

Ya rasu ya bar mata biyu da yara.

Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na BUK Rasuwa

A wani rahoton, tsohon shugaban rikon kwarya na Jami'ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Danjuma Maiwada, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.

Maiwada, wanda ya yi aiki na kankanin lokaci a matsayin shugaban riko na BUK a 2004, dan asalin Jihar Katsina ne amma mafi rayuwarsa a Kano ne inda ya ke koyarwa a jami'ar tun 1976 a tsangayar ilimi.

Kara karanta wannan

Tinubu, Dangote, Gwamnoni Da Sauran Manyan Masu Fada Aji Da Suka Halarci Auren Diyar Shettima

A shekarar 2015, ya yi aiki a matsayin shugaban riko na jami'an Northwest University, Kano da yanzu ake kira Jami'ar Yusuf Maitama Sule.

Yana daga cikin masu fada a ji a tsangayar koyar da manya da ilimin addinin musulunci kuma ya koyar da malamai ciki har da shugaban jami'an na yanzu, Farfesa Sagir Adamu Abbas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel