Uban 'Yan Sa'a: Wani Mutumi Ya Taki Sa’a, Ya Ci Naira Tiriliyan 1 a Wajen Caca

Uban 'Yan Sa'a: Wani Mutumi Ya Taki Sa’a, Ya Ci Naira Tiriliyan 1 a Wajen Caca

  • An shiga wata caca a Amurka, inda aka samu mutumin da ya yi nasarar tashi da kudin da sun kai $2.04bn
  • Zuwa yanzu babu wanda ya san sunan wanda ya taki wannan sa’a, amma nan gaba zai bayyana kan shi
  • Idan ya ga dama zai iya karbar biliyoyin a lokaci daya, idan kuma ya so zai iya karbarsu sannu-a-hankali

Abuja - Wani mutumi ya saye tikiti a kudancin Kalifoniya a kasar Amurka, a karshe hakan ya yi sanadiyyar da ya samu fam Dala biliyan 2.04.

Jaridar Daily Mail ta rahoto cewa a dokar Kalifoniya, dole wannan Bawan Allah ya bayyana kan shi.

Wanda ya samu nasarar ya saye tikitin ne a cibiyar Joe da ke Altadena a birnin Kalifoniya. Ya zama dole Duniya ta san shi da inda yake zama.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sace Dan Takarar Majalisa A Hanyarsa Na Zuwa Ganin Wakilan Akwatin Zabe

Jihohin da ake bada dama wanda ya ci caca ya boye kan sa a Amurka su ne: Kansas, Delaware, Maryland, Dakota, Ohio, Texas da Kudancin Carolina.

A karshe an samu mai kafar sa'a

A ranar Talata da ta gabata aka fitar da sunayen wadanda suka yi nasara a cacar da aka shiga, bayan an samu matsaloli a Litinin din da aka yi niyya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fito da sunayen asalin wanda ya yi nasara zai tabbatar da gaskiya, kuma mutane su gamsu akwai wanda zai yi nasara a gasar cacar da suka shiga.

Casino
Wajen caca Hoto: businesspost.ng
Asali: UGC

Haraji na jiran kudin da aka ci

Amma har zuwa yanzu ba a san sunan wannan mutumi ba tukuna. Wanda ya ci kyautar yana da damar ya raba kudinsa ko ya karbe su a lokaci guda.

Idan har ya karbe su a nan-take, Dala miliyan 518 za su iya tafiya wajen haraji.

Kara karanta wannan

Zai yiwu kuwa? Dan Najeriya ya ba da labarin yadda ya mutu kana ya dawo duniya

A wani bayani da aka fitar a shafin kamfanin cacar, an fahimci cewa wannan ne karon farko a tarihi da wani ya mallaki Dala biliyan 1 a wajen caca.

Mutanen Kalifoniya sun ji dadi ganin cewa daga cikinsu ne aka samu wanda ya samu nasara. Jaridun gida irinsu Vanguard sun fitar da rahoton nan.

Ba a san adadin tikitin da aka saida na shiga cacar ba, amma an saida tikiti miliyan 280 a ranar Asabar da ta wuce, wanda ya yi galaba ya tsira da biliyoyi.

Abin da hakan yake nufi shi ne wadanda suka saye tikitin cacar, sun zarce yawan mutanen da suka kara kuri’a a zaben majalisa da aka shirya a Amurka.

EFCC tayi nasara a kotu

Labari ya zo cewa Jonah Otunla da Kanal Bello Fadile sun rasa dukiyoyinsu a sakamakon nasarar da Lauyoyin EFCC suka samu a kansu a kotu.

Kara karanta wannan

Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

Otunla ya rike Akanta Janar a Najeriya yayin da shi Bello Fadile ya yi aiki da Kanal Sambo Dauki a NSA a lokacin Gwamnatin Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel