Borno: Tubabbun Yan Boko Haram Sunyi Aikin Tsaftacce Gari A Maiduguri, Sun Roki Mutane Su Yafe Musu

Borno: Tubabbun Yan Boko Haram Sunyi Aikin Tsaftacce Gari A Maiduguri, Sun Roki Mutane Su Yafe Musu

  • Wasu tubabbun yan Boko Haram sun yi aikin tsaftacce gari a wasu unguwanni a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a yau Asabar, suna rokon al'umma su yafe musu
  • Cibiyar Dimokradiyya da Ayyukan Cigaba, CDD, ce ta shirya atisayen tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Borno a wani mataki na shirin mayar da tubabbun yan ta'addan cikin al'umma
  • Mala Mustafa, wani babban mai bincike a CDD ya ce an shirya atisayen ne domin fara gina kyakyawan alaka da yarda da juna tsakanin tubabbun yan ta'addan da mutanen gari

Borno, Maiduguri - Wasu tubabbun yan ta'adda, a ranar Asabar, sun yi aikin tsaftacce unguwanni a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abuja: An kame wasu mutane 480 da ake zargin sun tsere daga magarkamar Kuje

A cewar kamfanin dillancin labarai, NAN, Cibiyar Dimokradiyya da Cigaba, CDD, tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno suka shirya atisayen.

Repentent Terrorist.
Borno: Tubabbun Yan Boko Haram Sun Tsaftacce Unguwanni, Sun Nemi Al'umma Su Yafe Musu. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikin tubabbun yan ta'addan sun saka riguna dauke da rubutu da ke cewa 'Don Allah ku yafe mana', 'Mun tuba', da 'Mu taru mu sake gina Borno'.

Da ya ke magana kan atisayen, Mala Mustafa, wani babban mai bincike a CDD, ya ce an yi atisayen don shirya mayar da su cikin mutane.

"Hikimar atisayen shine CDD ta tallafawa gwamnatin Jihar Borno a matsayin wani aiki na shirya mayar da tsaffin mayakan cikin al'umma," in ji Mustafa.
"Muna ganin akwai bukatar samu canji, musamman irin kyamatarsu da ake yi a cikin gari.
"Muna son gina alaka mai kyau da amintaka tsakanin wadanda suka mika wuya da mutanen gari."

Kara karanta wannan

Mutumin da aka daba wa wuka saboda batanci ga Annabi na can asibiti rai hannun rabbaba

Mustapha ya cigaba da cewa za a fadada atisayen zuwa wasu zababbun unguwanni a Maiduguri da garuruwa da ke makwabtaka da su, rahoton The Guardian.

Mashawarcin Gwaman Borno ya yi martani

A bangarensa, Abdullahi Ishaq, mashawarci na musamman ga gwamnatin Borno kan tsaro ya yaba da atisayen da CDD ta yi.

"CDD ta samar da kayayyaki yin wannan aikin kuma suna taimaka mana da shawarwari a matsayinsu na abokan hulda," in ji Ishaq.

Ya ce shirin da gwamnatin ta fara na tsawon shekara ya saka yan ta'adda da dama sun ajiye makamai, kuma ya taimaka wurin aikin dawo da zaman lafiya a Borno.

Ya yi kira ga sauran yan Najeriya da kungiyoyi su taimaka wurin cigaba da atisayen, wanda ya ce na bukatar kudi da wasu nau'in tallafin.

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda

A wani rahoton, Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno yayin da yake amsar tubabbun ‘yan ta’adda ya ce gwamnati ba za ta makance wa hadarorin da ke tattare da shirin sabunta dabi’un tsofaffin ‘yan ta’addan ba, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe: An kama wadanda ake zargin sun shiga ofishin gwamnan Katsina sun sace miliyoyi

A cewarsa, akwai bukatar tsananta tsaro da kuma bin hanyoyi da dama wadanda za su cire hadarorin da ke tare da shirin, kuma su tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel