2023: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Duƙa Gaban Wike, Ya Ya Roki Ya Goya Masa Baya

2023: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Duƙa Gaban Wike, Ya Ya Roki Ya Goya Masa Baya

  • Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya roki gwamna Wike ya taimaka ya goyi bayansa a 2023
  • A wurin kaddamar da gadar sama ta 9 da Wike ya gina, Obi yace zai barwa Wike Ribas, shi kuma ya mara masa baya
  • Wannan rokon na Peter Obi ya zo ne yayin da rikicin PDP ya hana gwamna Wike goyon bayan Atiku Abubakar

Rivers - Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar LP ya roki gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya marawa takararsa baya a 2023.

Mista Obi ya yi wannan rokon ne ranar Alhamis a wurin taron kaddamar da sabuwar Gadar sama Nkpolu Oroworukwo, a Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

Peter Obi da Wike
2023: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Duƙa Gaban Wike, Ya Ya Roki Ya Goya Masa Baya Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Mai neman zama shugaban kasa na Labour Partyn yace zai tabbata darajar Ribas ta ɗaga sama idan ya ci zaɓe a 2023, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Na Gano Matsalar Najeriya, Abu Ɗaya Ne Tal, Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Magantu

"Zan yi magana da mutane na zamu tattauna, idan muka goyi bayansa a jiha shi kuma zai mara mana baya a ƙasa. Zamu tattauna kan haka mun san kai ne Oga."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ba zamu yi gaddama da kai ba, duk wanda ya yi taƙaddama da kai bai san abinda yake ba. Ba zan fara ba, ina dai roko ka bamu wannan ka ɗauki ɗayan, zamu bar maka, na san yadda zan ja su a can."
"Ina baka tabbacin kudirin da muka sa a zuciyarmu na gina Najeriya, ba zamu ci gaba da tafiya a haka ba. Ni da Datti mune wakilan goben Najeriya. Na faɗa wa yan Najeriya su kama ni kan kowane abu, ba uzuri don na san matsalar."

- Peter Obi.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kuma yaba wa Wike bisa ɗumbin ayyukan alherin da yake zuba wa Ribas, Inda ya kara da cewa Patakwal ta isa zama cibiyar fitar kayayyaki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan PDP ya yi watsi da Atiku, ya zabi dan takarar da zai taimakawa a jiharsa 2023

Ina rokonka guiwowina a ƙasa - Obi

Obi ya shawarci Wike ya tsaya kan tsarukansa duk rintsi Kuma yace idan gwamnan Ribas ya goyi bayan LP to damar lashe zaɓe zata ƙaru a 2023.

"Karka manta da wannna yarjejeniyar ta yau, na duƙa kan guiwa ina rokonka, ka rike wannan ka barmun ɗayan, ina baka tabbacin wanda zan ɗauka zan ɗaga Ribas ta zarce haka."

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa rokon Obi na zuwa ne yayin da rigingimu suka addabi PDP, lamarin da ya hana Wike goya wa Atiku Baya.

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya jaddada bukatun da za'a tafi a kansu mataukar ana son yin sulhu a jam'iyyar PDP

Gwamnan yace mambobin jam'iyyar na yanzu sune a baya suke yabonsa ba dare ba rana amma don kawai yace a gyara ba dai-dai ba har ya zama maƙiyi.

Jagoran gwamnonin G5 yace burinsu kawai a gyara fasali a yi dai-daito, adalci da gaskiya, wannan ne kaɗai bukatunsu kafin a yi sulhu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel