Sojoji Sun Kashe Wani Dansanda Bayan Sun Lakada Mishi Dukan Tsiya A Legas

Sojoji Sun Kashe Wani Dansanda Bayan Sun Lakada Mishi Dukan Tsiya A Legas

  • Wasu fusatattun sojoji sun lakadawa wani dan sanda duka inda suka kashe har lahira a wani hari da suka kai kan babbar hanyar Mile 2 dake jihar Legas
  • Sojoji Sun Far wa jami'an Yansanda bayan sun tsayar da su a yayin da suka gyara cunkosun ababen hawa akan babbar hanya a Legas
  • Hukumomin Yansanda da na rundunar sojoji sun bayyana rigima tsakanin jami'an yansanda da sojoji a matsayin abin takaici

Jihar Legas - Wasu fusatattun sojoji sun lakada wa wani dan sanda duka inda suka kashe har lahira a wani hari da suka kai kan babbar hanyar Mile 2 Badagry a jihar Legas a ranar Laraba. Rahoton Daily Trust

Dan sandan da ya rasu ya kasance Insifeto ne da ke aiki da sashen Ojo na rundunar ‘yan sandan jihar Legas.

Kara karanta wannan

An kama Wasu ‘Yan Sanda Biyu Da Zargin Cire Ma Wani Dilan Kayan Mota Miliyoyin Kudi a POS

Sojoji ne suka kai wa jami’in da abokan aikinsa hari a lokacin da suke gyarar cunkoson ababen hawa a kan babbar hanyar.

An gano cewa sojojin da ke dawowa daga wani kwas sun fusata ne a lokacin da aka tsayar da layinsu domin baiwa sauran masu amfani da hanyar damar wucewa.

Wani ganau mai suna Sule Abiodun, ya ce sojojin sun dira daga motarsu, inda suka kama ‘yan sandan suka tafi da su.

Sule yace daga baya sun ji labarin cewa sojojin sun yansandan barikinsu inda suka musu dukan tsiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sojoji
Sojoji Sun Kashe Wani Dansanda Yayin Da Suka Lakadawa Mishi Dukan Tsiya A Legas FOTO Legit.ng
Asali: Twitter

Wani shaida kuma ya yi zargin cewa sojojin sun yi yunkurin jefar da gawar marigayin ne a wani magudanar ruwa da ke kusa da wurin, amma jami’an sojin da ke kula da barikin suka hana su.

Har yanzu dan sanda na biyu yana kwance a asibiti yayin da aka ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawa

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Arewa Mazauna Jihar Imo Tare da Filewa Mutum Daya Kai

Sai dai hukumomin ‘yan sanda da na runduna Soji ta bataliya 81 na Najeriya sun bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya wallafa a shafinsa na Twitter game da lamarin .

Shima da yake mayar da martani kan lamarin, mataimakin daraktan hulda da jama’a na shiyya ta 81 na rundunar sojin Najeriya, Olaniyi Osoba, ya ce tuni hukumar da ke kula da sashen ta tuntubi manyan jami’an ‘yan sanda a jihar domin shawo kan lamarin.

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Google Ta Hana IPOB Shiga Dandalin Ta

A wani labari kuma, Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Alhamis ya roki kamfanin Google da ta hana mambobin kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB) damar amfani da dandalinta. Rahoton Daily Trust

Da yake magana jiya a Abuja a lokacin da wata tawagar Google ta ziyarce shi, ya ce:

Asali: Legit.ng

Online view pixel