Zaman Tinubu Da CAN: Zai Yi Wuya Tinubu Ya Yi Biyan Bukatu 2 cikin 7 Da CAN Ta Gabatar

Zaman Tinubu Da CAN: Zai Yi Wuya Tinubu Ya Yi Biyan Bukatu 2 cikin 7 Da CAN Ta Gabatar

  • Har yanzu tsugunnu bata karewa Tinubu ba kan yunkurin shawo kan kungiyar kiristocin Najeriya CAN
  • Kungiyar tun farko ta nuna rashin amincewarta da Tinubu saboda ya zabi abokin tafiya Musulmi
  • Bayan zama da shi ranar Laraba, ta gabatar masa da jerin bukatu 7 da take son yayi mata alkawarin cika

A ranar Laraba, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta ce saura kwanaki 100 cir a gudanar da zaben shugaban kasan Najeriya.

Wanda ya lashe zaben Febrairu 2023 ne zai gaji kujerar shugaba Muhammadu Buhari wanda wa'adinsa na biyu ya zo karshe.

Sakamakon haka yan siyasa masu dakon mallakar kujerar sun bazama yakin neman zabe.

A cikin wannan yunkuri, dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyya mai ci, APC, Bola Ahmed Tinubu, ya zanna da kungiyar Kiristocin Najeriya CAN.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Da farko CAN karkashin Rabaran Ayokunle ta lashi takobin cewa babu abinda zai hada ta da Tinubu saboda ya zabi mataimaki Musulmi.

Amma sabuwar gwamnatin CAN karkashin Daniel Ukoh ta gayyaci Tinubu don tattaunawa da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A zaman da sukayi ranar Laraba a Abuja, CAN ta gabatarwa Tinubu bukatu bakwai.

Sun hada da:

1. Yan sandan jiha ko kuma rundunar yan sanda wacce ba tarayya ke kula da ita ba

2. Ba wa jihohi karfin iko

3. Daidaito da bawa dukkan addinai hakokinsu

4. Ba wa dukkan kabilu ikon cin gashin kansu

5. Ba wa garuruwa ikon kula da albarkatunsu

6. Rashin amincewa da kiwo a fili

7. Tsarin zabe wanda zai ba wa kowa damar yin zabe da kuma a zabe shi/ita

Legit ta yi dubi da ainul basira cikin wadannan bukatu bakwai.

Kara karanta wannan

2023: APC ta samu karin karfi, wasu jiga-jigan sarakuna sun ce suna goyon bayan Tinubu

Da farko dai biyu cikin wadannan bukatu da kamar wuya ya iya biya, yayinda 2 tuni akwai su a kundin tsarin mulki, sauran 3 kuwa aikin majalisa ne.

Tinubu
Zaman Tinubu Da CAN: Zai Yi Wuya Tinubu Ya Yi Biyan Bukatu 2 cikin 7 Da CAN Ta Gabatar Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Bukatu Biyu Da Tinubu Ba Zai Iya Biya Ba

1. Ba wa dukkan kabilu ikon cin gashin kansu

Biyan wannan bukata na nufin cewa za'a kacaccala Najeriya gida-gida kuma yan kungiyar rajin ballewar daga Najeriya sun samu nasara.

Wannan bukata da kamar wuya Tinubu ya iya biya saboda ya bayyana cewa shi ya fi ganin amfanin kasancewar Najeriya daya fiye da rabuwa.

Yan kabilar Igbo dai tun zaman Yakubu Gowon suke neman ballewa daga Najeriya, wanda hakan yayi sanadiyar yakin basasa a 1967.

2. Ba wa garuruwa ikon kula da albarkatunsu

Duk da cewa baiwa jihohi ikon kula da mallakar albarkatun cikin kasa na daya daga cikin abubuwan da shawarar yi idan za'a yi garambawul, amma wannan ba hurumin shugaban kasa ba bane.

Kara karanta wannan

"Mazi Tinubu": Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Ya Samu Sarauata A Yankin Su Peter Obi

Ana bukatar amincewar mafi akasarin yan majalisar dokokin tarayya da jihohi kafin hakan ya yiwu.

Yan majalisa da yawa kuwa ba zasu amince da wannan ba saboda ana ganin wasu jihohi musamman masu arzikin man fetur zasu fi amfana da shi fiye da marasa arzikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel