Zaben 2023: Limamai Za Su Yi Wa Ƴan Takarar Gwamna A Kaduna Tambayoyi Kan Manufofinsu

Zaben 2023: Limamai Za Su Yi Wa Ƴan Takarar Gwamna A Kaduna Tambayoyi Kan Manufofinsu

  • Limamai da malaman addinin musulunci a Kaduna za su shiryawa yan takarar gwamna a zaben 2023 wani taro
  • Imam Musa Tanimu, sakataren kungiyar limaman ya ce dalilin kiran taron shine sanin manufofi da yan takarar suka tanada wa jihar, saboda al'umma su yanke shawara wanda za su zaba
  • Tanimu, ya ce limaman ba su da wani dan takara da suka goyon baya, kuma ya yi kira ga yan siyasa su yi kamfen mai tsafta

Kaduna - Kwamitin limamai da malamai na Jihar Kaduna ta ce bayana shirinta na tattaunawa da yan takarar gwamna a jihar don bawa al'ummar musulmi damar fahimtar shirye-shirye da kowannensu ke da shi, rahoton Daily Trust.

Mataimakin sakataren kwamitin, Imam Musa Tanimu, yayin jawabin da ya yi wurin taron manema labarai a ranar Laraba, ya ce dalilin taron shine nusantar da mambobinta kan bukatar zaben shugabanni masu gaskiya da rikon amana da za su mulki jihar.

Kara karanta wannan

Satar N800m: An kama tsohon dan takarar gwamna yayin da yake shirin tserewa a Abuja

Taswirar Kaduna
2023: Limamai Za Su Tattauna Da Yan Takarar Gwamna A Kaduna Don Sanin Manufofinsu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba mu da dan takara da muke goyon baya - Tanimu

Amma ya fayyace cewa kwamitin ba da ta wani dan takara da ta take goyon baya, ya kara da cewa:

"Mun shirya taron tattaunawar ne don mambobinmu su fahimci inda dukkan yan takarar suka dosa, su kuma yanke shawara mai kyau."

A cewarsa, tun da farko kwamitin ta janyo hankulan yan siyasa su guji furta maganganun da za su kawo rashin hadin kai tsakanin musulmi da al'umma baki daya.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, ya ce mafi yawancin mambobin kwamitin limaman masallatan Juma'a ne da ke mutane a kalla 200 da ke sallah a masallatan su.

A cewarsa:

"Suna da hanya mai sauki na haduwa da jama'a tare da isar da sakonni masu kyau ta hanyar tattauna abin a hudubarsu."

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Kwankwaso Ya Fallasa Asirin Gwamnoni na Satar Dukiyar Talakawa

Ya yi kira ga dukkan yan takarar su taho su sanar da mutane shirye-shiryensu yana mai jadada cewa, "kwamitin ba ta goyon bayan kowanne dan takarar, kawai tana bawa kowa dama ne."

Ya yi kira ga yan siyasa su yi kamfen ba tare da tada hankula ba ko rikici ko furta maganganun da za su janyo tabarbarewar doka da oda.

El-Rufai Ya Tuna da Irin Rashin Mutuncin da Peter Obi Ya Yi Masa a 2013

Malam Nasiru El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna,ya bayyana a wani faifan bidiyon da TVC ta yada, inda yake bayyana kadan daga abu mara dadi da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya yi masa.

Ya tuna cewa, a shekarar 2013, ya kai ziyarar duba zabe a jihar Anambra, a nan ne dai Obi ya tsare shi tare da kokarin tozarta shi don a lokacin baya rike da mukamin gwamna.

Kara karanta wannan

Magana ta dawo baya: Ba Mu Yanke Ranar Dawo da Jirgin Kaduna-Abuja ba – NRC

Asali: Legit.ng

Online view pixel