Majalisar Dattawa Ta Najeriya Ta Goyi Bayan CBN Akan Sake Fasalin Naira

Majalisar Dattawa Ta Najeriya Ta Goyi Bayan CBN Akan Sake Fasalin Naira

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya samu sahhalewar majalisar dattawa kan yunkurin sake fasalin Naira
  • CBN ya bayyana sauya N200, N500 da N1,000 nan da wani lokaci, lamarin da ya girgiza 'yan Najeriya
  • Daraktan kudi na CBN ya yi tsokaci kan yadda sake fasalin zai kasance, da kuma warware wasu batutuwa da dama

FCT, Abuja - Majalisar dattawa a ranar Laraba 16 ga watan Nuwamba ta bayyana goyon bayanta ga manufar babban Najeriya (CBN) na sake fasalin kudin Najeriya, The Nation ta ruwaito

Wannan na zuwa ne daga shawarin da majalisar ta yi ta bangaren shugaban kwamitinta kan harkokin banki, inshora da hada-hadar kudi, Sanata Sani Uba.

Yayin da ta amince da sake fasalin, ta kuma yi tsokaci da cewa, karshen watan Janairu ya yi kusa ga mayar da kudaden da ke yawo a kasar zuwa banki.

Kara karanta wannan

2023: Shugaba Buhari ya fadi babban abin da zai yi kafin ya sauka a mulki

Majalisa ta sahhalewa CBN aikin sake fasalin Naira
Majalisar Dattawa Ta Najeriya Ta Goyi Bayan CBN Akan Sake Fasalin Naira | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A tabbatar an wayar da kan jama'a, kuma basu yi asara ba - Majalisa dattawa ga CBN

Majalisar ta yi kira ga CBN da ya yi aikin wayar da kan jama'a, musamman a yankunan karkara domin tabbatar da 'yan Najeriya sun san da sabuwar dokar mayar da kudade banki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa, hakan ne zai taimakawa 'yan Najeriya mazauna karkara su san halin da ake ciki don kaucewa tafka asara bangarensu, Channels Tv ta ruwaito.

Ta kuma bukaci CBN da ya tabbatar da saukaka hanyoyin hada-hadar kudi na zamani domin ba da dama ga 'yan kasa su shigar da kudaden banki a lokacin da aka ayyana.

Hakazalika, majalisa ta nemi CBN ya tabbatar tsaron jama'ar da za su dauko kudadensu daga nesa, musamman ganin yadda ake yawan samun ta'addanci a kasar nan.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: CAN za ta yi wata zama da 'yan takarar shugaban kasa saboda wasu dalilai

Daga karshe ta nemi bankin ya samar da hanyoyin da za su tabbatar da 'yan ta'adda basu samu damar shigar da kudaden da ke hannunsu ba.

Ba za a cire rubutun Ajami a jikin kudi ba, inji daraktan kudi na CBN

Daraktan kudi na CBN, Ahmed Bello Umar ya yi karin haske kan batun da ake yadawa na cewa bankin zai cire rubutun Ajami a jikin sabbin kudi.

Wasu kalilan daga 'yan Najeriya sun yi ta kira a cire rubutun a jikin kudi, yayin da wasu ke kira da barin rubutun; kowa ya fadi dalili.

Daraktan ya yi bayani, ya bayyana yadda aikin sake fasalin wasu kudade na Najeriya ke tafiya a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel