An Umarci Wani Mutum da Ya Share Harabar Kotu Saboda Laifin Satar Turare

An Umarci Wani Mutum da Ya Share Harabar Kotu Saboda Laifin Satar Turare

  • An umarci wani matashi da ya share harabar kotu bisa laifin satar turare a wani kantin siyayya a Abuja
  • Mai shari'a Malam Ishaq Hassan ya hukunta matashin ne bayan da ya amsa aikata laifin tare da yi masa gargadi
  • Ba wannan ne karon farko da ake yiwa matasa hukunci mai ban mamaki irin wannan ba a Najeriya bisa aikata kananan laifuka

Garki, Abuja - Wani alkali, Malam Ishaq Hassan a ranar Talata ya umarci wani matashi mai shekaru 24, Valentine Nmoye da ya ya share harabar kotun Karu a Abuja na tsawon sa'o'i uku bisa laifin satar turaren N4,000 daga wani kantin siyayya.

Hassan ya ba da wannan umarnin ne yayin da matashin ya amsa laifinsa na sata, ya kuma gargadi matashin da ya daina aikata mummunar dabi'ar sata, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hotunan Yadda Gobara Ta Laƙume Dukiyoyin 'Miliyoyi' A Kasuwar Singer Ta Kano

A tun farko, dan sanda mai shigar da kara, Olarewaju Osho ya shaidawa kotun cewa, Sadiq Ahmed na Tahalid Stores da ke Garki a Abuja ya kai karar matashin ga ofishin 'yan sandan Garki.

Kotu ta umarci matashi ya share kotu na awa 3 a Abuja bisa satar turare
An Umarci Wani Mutum da Ya Share Harabar Kotu Saboda Laifin Satar Turare | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Osho ya bayyana cewa, an zargi matashin ne da laifin shiga kantin ne tare da sace turare guda uku da kudinsu ya kai N4,000.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin bincike, Osho ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin da ya aikata, haka nan jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya ce abin da ya aikata laifin a dokar Panel Code sashe 287.

Ba wannan ne karon farko da ake yankewa matasa hukuncin shara ba a kotun Najeriya, hakan ya sha faruwa a wasu jihohin Arewacin Najeriya.

An yankewa mata hukuncin share makarantar da danta yake karatu a Ogun

Kara karanta wannan

Satar N800m: An kama tsohon dan takarar gwamna yayin da yake shirin tserewa a Abuja

A wani labarin kuma, wata kotun majistere a jihar Ogun ta umarci wata mata da ta share harabar makarantar da danta yake karatu bisa laifin tada zaune tsaye a makarantar sakandare da ke Iju-Ebiye a jihar.

Majiya ta bayyana cewa, an gurfanar da matar mai aure ne bayan da tazo makarantar ta tada hankalin malamai bisa zargin sun daki danta.

Mai shari'a Shotunde Shotayo, ya umarci matar mai suna Biola Joshua da ta fara shara tun karfe 8 zuwa 11 na safe a kullum na tsawon na tsawon watanni shida a matsayin ladabtarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel