Dan kuka: Mata za ta share harabar makarantar su danta na tsawon watanni 6 bisa laifin jibgar malami

Dan kuka: Mata za ta share harabar makarantar su danta na tsawon watanni 6 bisa laifin jibgar malami

  • Wata mata ta fuskanci fushin alkali saboda kokarin tada zaune tsaye a wata makarantar akaranta na tsawon watanni 6 saboda biyewa dantasakandare a Oyo
  • Wannan lamari dai ya je gaban kotu, inda masu gabatar da kara suka bayyana shaidu karara kan matar da danta
  • Bayan sauraran batutuwa, alkali ya gamsu da hujjoji, ya yanke mata hukunci duk da cewa ta musanta zargin

Oyo - Wata Kotun Majistare da ke Ota, Ogun a ranar Laraba ta umurci wata matar aure mai suna Biola Joshua ‘yar shekara 40 da ta share harabar makarantar sakandare ta Iju-Ebiye na tsawon watanni shida saboda kwasi ‘yan daba zuwa makarantar da danta ke karatu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, ‘yan sandan sun gurfanar da Biola da laifin hada baki, kai hari da kuma tada zaune tsaye a harabar makaranta.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane za su rasa aikin yi yayin da Naira ta kara durkushewa kasa a kasuwar canji

Ta gamu da fushin kotu saboda cin zarfin shugaban makaranta
Dan kuka: Mata za ta share makarantar su danta tsawon watanni saboda barna | Hoto: vanguardngr.com

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Shotunde Shotayo, ya umarci matar da ta ke share makarantar daga karfe 8 na safe zuwa 11 na safe a kowace rana.

Ya kuma ba da umarnin cewa makarantar ta samu littafin sanya hannu ga matar inda za a rubuta ayyukanta na yau da kullum na tsawon watanni shida.

Shotayo ya bai wa Biola Joshua zabin biyan tarar N30,000 da za a ba shugaban makarantar da malamin da lamarin ya shafa.

Alkali ya ce masu gabatar da kara sun kawo shaidu kwarara da ke nuna ba shakka cewa Biola ta aikata laifin da ake tuhumarta akai.

A bangare guda, matar ta musanta zargin da ake mata a gaban alkali.

Yadda lamarin ya faru daga bakin mai gabatar da kara

Kara karanta wannan

Yadda aka gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8

Tun da farko, mai shigar da kara, Insp Cynthia Ejezie, ta shaida wa kotun cewa matar da danta da wasu mutane, sun aikata laifin ne a ranar 11 ga Maris, 2021, da misalin karfe 2 na rana a makarantar da ke Ota.

Ejezie ta ce, matar da abokan aikinta sun ci zarafin shugaban makarantar da jami’in lafiya na makarantar, inda suka ji raunuka a jikinsu, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ta kara da cewa, sun kuma nuna kansu ta hanyar da za ta haifar da rashin zaman lafiya ta yayin da suka mamaye makarantar tare da tada hankalin kowa.

Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 249(d),355 da 516 na kundin laifuffuka na jihar Oyo.

Kotu ta yankewa barawon Al-kur'ani hukucin sharan masallaci na kwanaki 30 a Kano

A wani labarin, wata kotun shari’a da ke zama a Fagge 'Yan-Alluna a Kano ranar Talata 17 ga watan Agusta ta umarci Halifa Abdullahi da ya share masallacin Juma’ar Fagge na tsawon kwanaki 30 a jere a matsayin hukuncinsa na satan kwafin Alkur’ani mai girma guda takwas.

Kara karanta wannan

Jibgegiyar Matata Tana Lakaɗa Min Duka Kuma Bata Nadama, Miji Ɗan Shekara 60 Ya Roƙi Kotu Ta Kashe Aurensa

Mista Abdullahi, mazaunin unguwar Yola da ke cikin birnin Kano, an zarge shi da sata a masallaci a unguwar Tudun Maliki ranar Lahadi da daddare tare da kwashe kwafin Alkur'ani guda takwas.

Sai dai jami'an tsaron masallacin sun cafke wanda ake zargin bayan ya aikata laifin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel