Mun Kafa Tawagar da Za Ta Bincika Harin da Aka Kai Kan Tawagar Atiku a Borno

Mun Kafa Tawagar da Za Ta Bincika Harin da Aka Kai Kan Tawagar Atiku a Borno

  • Sufeto janar na hukumar 'yan sandan Najeriya ya bayyana abin da rundunarsa ke yi kan harin da aka kai tawagar Atiku a Borno
  • Wasu 'yan daba sun yi kaca-kaca da ayarin motocin kamfen na dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar
  • Jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai, ta kuma zargi jam'iyyar APC da kitsa wannan mummunan aiki na ta'addanci

FCT, Abuja - Bayan labarin da aka samu na harin da aka kai kan tawagar dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar a jihar Borno, hukumar 'yan sanda ta yi martanim ta fadi matakin da ta dauka.

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba ya bayyana cewa, rundunar 'yan sanda ta kafa kwamitin da zai binciki wannan barna da aka yiwa dan takarar PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a taron ministoci na 57 da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, Channels Tv ta ruwaito.

Da yake jawabi game da farmakin, IGP Alkali ya ce, ya zuwa yanzu dai bayanai da hukumar ta samu daga Borno basu karasa kankama ba, don haka ya kirkiri kwamitin bincike don gano yadda gaskiyar abin da ya faru.

IGP Alkali Baba ya fadi abin da 'yan sanda ke yi bayan farmakar tawagar Atiku
Mun Kafa Tawagar da Za Ta Bincika Harin da Aka Kai Kan Tawagar Atiku a Borno | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa, rundunar dama takan tura jami'ai wuraren kamfen kuma suna ba da cikakken tsaro, musamman idan aka samu bayanai tun kafin fara taron.

A bangare guda, ya gargadi 'yan siyasa da su zama masu bin doka da oda a matsayinsu na shugabannin gobe, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Yadda aka farmaki tawagar Atiku a Borno

Idan baku manta ba, a ranar Laraba ne wasu 'yan daba suka farmaki tawagar kamfen dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a garin Maidguri, inda aka jikkata magoya bayansa.

Kara karanta wannan

PDP ta tona sirri, ta fadi dalilin da yasa 'yan APC suka farmaki tawagar Atiku a Borno

Rahotanni sun bayyana yadda kuma aka lalata motoci da dama a harin, lamarin da ya fusata mambobin PDP.

Jam'iyyar PDP ta yi Allah-wadai da wannan barna da aka yi kan dan takararta, kana ta nemi IGP da ya gaggauta daukar mataki a kai.

Jam'iyyar PDP ta daura alhakin wanna hari kan jiga-jigan APC, inda tace APC na hasada da karbuwar Atiku a yankin Arewa maso Gabas ne.

Hakazalika, ta roki shugaban 'yan sandan da ya yi kira ga jam'iyyun siyasa da su kasance masu son zaman lafiya da yada ta a lokacin kamfen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel