Hotunan Yadda Gobara Ta Yi Mummunan Ɓarna A Sashin NOUN A Jigawa

Hotunan Yadda Gobara Ta Yi Mummunan Ɓarna A Sashin NOUN A Jigawa

  • Gobara ta tashi a sashin jami'ar karatu daga gida wato NOUN da ke Jami'ar Tarayya ta Dutse, FUD, jihar Jigawa
  • Gobarar ta lakume abubuwa da dama da suka hada da kayan cikin ofis da wasu abubuwa a sashin
  • Hadakar jami'an kwana-kwana na jihar Jigawa da na tarayya da wasu ne suka yi nasarar kashe wutan

Jigawa, Dutse - Gobara ta cinye sashin Jami'ar karatu daga gida ta Najeriya, NOUN, da ke Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Daily Trust ta rahoto cewa gobarar wacce ta faru a ranar Asabar 12 ga watan Nuwamban 2022 ta lalata kayayyakin ofis da wasu abubuwa a sashin.

Gobara a NOUN Jigawa
Hotunan Yadda Gobara Ta Yi Mummunan Ɓarna A Sashin NOUN A Jigawa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Hukumar kwana-kwana na jihar da ta tarayya da Dutse International Fire Service ne suka taru suka kashe gobarar, rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Babban Jigon PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC a Wata Jahar Arewa

Kawo yanzu ba a tabbatar da musababin tashin gobarar ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga hotunan a kasa:

Gobara a NOUN
Hotunan Yadda Gobara Ta Yi Mummunan Ɓarna A Sashin NOUN A Jigawa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gobara ta NOUN
Gobara a NOUN Jigawa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gobara a NOUN
Barnar da gobara ta yi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gobara a NOUN a Jigawa
Gobara ta yi barna a ginin NOUN a Jigawa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Hotuna: An Yi Gobara A Majalisar Tarayyar Najeriya, Kayayyaki Sun Kone

Gobara ta lashe wani daki a ginin majalisar tarayyar Najeriya da ke birnin tarayya a Abuja, Leadership ta rahoto.

Gobarar ta faru ne a yammacin ranar Alhamis a bene na biyu, daki na 227, a sabon bangaren majalisar wakilai na tarayya.

A cikin sanarwa da ya fitar a daren ranar Alhamis, Agada Emmanuel, direktan watsa labarai na majalisar tarayya, ya ce ana zargin matsalar lantarki ya janyo gobarar, The Punch ta rahoto.

Gobara Ta Kama Majalisar Dokokin Jihar Kogi a Yau Litinin

A wani rahoton, kun ji cewa zauruka da farfajiyar majalisar dokokin jihar Kogi sun kama da wata gobara, inji wani rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Yi Fatali da Wanda Ya Ci Zabe, Ta Bayyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC a Wata Jiha

Ya zuwa yanzu dai ba a san sanadiyyar kamawar wannan mummunan gobara ba da ta tashi a yau Litinin 10 ga watan Oktoba.

Kakakin majalisar dokokin jihar ta Kogi, Prince Mathew Kolawole ya shaidawa manema labarai cewa, hukumomi za su binciki lamarin.

Hakazalika, daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Salau Ozigi ya ce gobarar bata tsallaka zaurukan majalisar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel