Zamfara: Sojoji Sun Ceto Wadanda Aka yi Garkuwa dasu, Sun Samo Makamai da Babura

Zamfara: Sojoji Sun Ceto Wadanda Aka yi Garkuwa dasu, Sun Samo Makamai da Babura

  • Dakarun Operation Forest Sanity dake jihar Zamfara sun samu nasarar ceto wasu mutum uku daga masu garkuwa da mutane bayan sun je sintiri maboyarsu
  • Sojojin sun garzaya har kauyen Danmarke dake karamar hukumar Gummi inda suka sakarwa sojojin wuta wanda hakan yasa suka arce da raunikan bindiga
  • Sojojin sun kakkabe maboyar inda suka samo mutum 3, harsasai layi da babura duk mallakin ‘yan ta’addan da aka ragargaza

Zamfara - Dakarun sojin rundunar Operation Forest Sanity sun ceto wasu mutane da aka yi garkuwa dasu a jihar Zamfara.

Dakarun Soji
Zamfara: Sojoji Sun Ceto Wadanda Aka yi Garkuwa dasu, Sun Samo Makamai da Babura. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kamar yadda daraktan yada labarai na tsaro, Manjo janar Musa Danmadami ya fitar a wata takarda, dakarun wadanda a ranar Alhamis suka fita sintiri har zuwa maboyar ‘yan bindiga a kauyen Danmarke dake karamar hukumar Gummi ta jihar, sun samo har da wasu makamai.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar Gwamnan PDP na Borno Ya Fallasa Yadda Harin da Aka Kaiwa Tawagar Atiku Ya Faru

An ceto mutum 3 da aka yi garkuwa dasu

Janar Danmadami yayi bayanin cewa dakarun sun yi arangama tare da yin musayar wuta da ‘yan ta’addan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A yayin artabu da ‘yan ta’addan, sun tsere tare da barin maboyarsu amma sun sha ne da kyar da miyagun raunikan bindiga. Dakarun sun duba yankin tare da ceto wasu mutum 3 da aka yi garkuwa dasu. An samo bindigogi kirar AK47 guda biyar tare da babura talatin da sauransu.”

Mai magana da yawun hedkwatar tsaron ya bayyana cewa hukumar sojin ta yabawa dakarun Operation Forest Sanity tare da kara wa jama’a karfin guiwa kan su samarwa dakarun bayanai masu inganci kuma a kan lokaci a duk inda aka ga wani abin laifi.

Zamfara ta zama sansanin ‘yan bindiga

Jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya tayi kamari tare da suna a bangaren rashin tsaro wanda hakan ya janyo asarar rayuka da kadarorin jama’a

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga Sun Halaka Mutum 2, Sun Tarwatsa Kauyuka 10 a Kano

Manoma da yawa sun tafka asara tun bayan bullar rashin tsaro a yankin.

A wasu lokuta, yan ta’addan kan kallafa haraji a kan Manomi inda suka biya domin samun noma gonakinsu.

A kuwa yankunan da abun yayi kamari, ‘yan ta’addan na hana noma ko kuma su sanyawa amfanin gonar wuta ya kone kurmus bayan da manoman suka gama aiki yayin da suke jiran girbe amfanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel