Takalmi Mai Siffar Kafar Mutum da Kaho Ya Tada Kura a Kafar Sada Zumunta

Takalmi Mai Siffar Kafar Mutum da Kaho Ya Tada Kura a Kafar Sada Zumunta

  • Wani bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta na wani takalmi mai ban mamaki, ya yi kama da kafar dan adam sak
  • Takalmin sau ciki mai launin fatar mutum yana kuma wani kaho a ijikinsa, ga kuma burmin yatsu kana yana da tudu
  • Bidiyon da aka yada da sunan kwalliya a kafar sada zumunta, ya bar jama'a da dama cikin mamaki

Idan aka zo maganar gayu da kuma kwalliya, babu kalar hauka da ba za a gani ba, domin kuwa mutane kan wuce iyaka wajen nuna kwarewar basirarsu.

Wani bidiyo da aka yada a intanet bai sauya zane ba, domin kuwa ya dauki wata siffa mai ban mamakin gaske.

A bidiyon da @lessiswore ya yada a Instagram, an nuna wani dan kwalisan takalmi ban siffar kafar dan adam ga kuma launin jiki kamar dai fatan mutum.

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Cikin Makonni 2 Da Sanarwa, Jama'a Sun Kai Kudi N52bn Bankuna

Takalmin da ya ba da mamaki a kafar intanet
Takalmi Mai Siffar Kafar Mutum da Kaho Ya Tada Kura a Kafar Sada Zumunta | Hoto: @lesisworewomen
Asali: Instagram

Takalmin mai tudu an ganshi da tsini, ga kuma kwalmada da siffar kafa daidai inda mutum zai tura kafa ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Mutane da dama a shafin Instagram sun yi martani mai daukar hankali bayan ganin wannan sabon nau'in takalmi mai cike da abin al'ajabi.

tryabreathmint:

"Wannan abin ban tsoro ne ai."

yngmorning:

"Wannan shine abu mafi ban tsoro da na gani a wannan watan. Nagode."

ataleofjoy:

"Wannan karshe kenan."

lebrieg:

"Wannan ba zai yiwu ba."

reesesaleh:

"Tabbas ba zan saka wannan ba."

the_celestialgodus:

"Na tsorata, kuma na ji kyamarsa, Ban san ya na ji game da wannan ba."

mr.willl__:

"Wannan ya yi kama da abubuwan da Kanye West zai iya kawo wa kamar dai yadda yake."

sophiemolhoek:

"'Yan matan da za su iya siya za su siya, wadanda ba za su iya ba ba za su iya ba."

Kara karanta wannan

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

Budurwa ta yada bidiyon takalmin da neman aurenta yazo dashi

A wani rahotonmu na baya, wata budurwa ta yada bidiyon wani kalan takalmi da mutumin da ya zo neman aurenta.

An ga wani mataccen takalmi da bai kamata mutum ya saka yya tafi ganin surukai ba, lamarin da ya ba jama'a mamaki kwarai da gaske.

Mutane sun shawarci budurwar kan wannan takalmi da ta yada a Tiktok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel