Anambra: ‘Yan Sanda Sun Dakile Harin Fashi da Makami Kan Motar Banki

Anambra: ‘Yan Sanda Sun Dakile Harin Fashi da Makami Kan Motar Banki

  • ‘Yan ta’adda da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai mummunan farmaki kan motar kudi dake tafe tare da jami’an tsaro
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra CP Echeng Echeng, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace ‘yan sanda sun dakile lamarin
  • Ya sanar da cewa lamarin ya faru wurin karfe 4 na yammacin Laraba a Ufoma dake karamar hukumar Orumba ta kudu a jihar Anambra

Anambra - Wasu ‘yan ta’adda da har yanzu ba a gane ba su ba sun kai wa motar kudi farmaki a Ufuma, karamar hukumar Orumba ta Kudi a jihar Anambra, jaridar The Punch ta rahoto.

‘Yan sanda
Anambra: ‘Yan Sanda Sun Dakile Harin Fashi da Makami Kan Motar Banki. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

An tattaro cewa lamarin ya faru a ranar Alhamis yayin da motar kudin ke kai tsabar kudi wani wuri da ba a bayyana ba.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar Gwamnan PDP na Borno Ya Fallasa Yadda Harin da Aka Kaiwa Tawagar Atiku Ya Faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan ta’addan sun bibiyi motar kudin da jami’an tsaro zuwa yankin kauyen Ufuma tare da bude wuta kan motar tare da jami’an tsaron dake tafe da ita.

Wani ganau yace:

“Lamarin ya faru a ranar Alhamis wurin karfe 5 na yamma kuma an dinga jin harbe-harbe babu kakkautawa.
“Dukkan mazauna yankin sun tsere yayin da jami’an tsaron dake tare da motar kudin suka yi artabu da ‘yan fashin. ‘Yan sandan sun yi nasarar dakile farmakin.”

Yan Sanda sun magantu kan farmakin

A yayin tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, yace lamarin ya faru wurin karfe 4 na yamma amma cike da nasara aka fatattaki ‘yan fashin.

Ikenga yace an kama wasu motoci kirar Lexus Jeep da Highlander mallakin ‘yan fashin inda ya kafa da cewa an samo harsasai, rigar da harsashi baya hudawa, layu da wasu kayayyaki.

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

“Jami’an dake tare da motar kudin sun yi kokarin dakile farmakin. Lamarin ya faru wurin karfe 4 na yammaci a Umunebo dake Ufuma.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Echeng Echeng tuni yayi umarnin fara bincike tare da nemo maharan. An kama ababen hawan ‘yan fashin.”

- Yace.

Ba wannan bane karon farko

Ba wannan bane karo na farko da ‘yan ta’adda ke kai farmaki kan motocin banki tare da wawushe kudaden.

Sai dai sau da yawa a kan yi artabu da jami’an tsaro wurin dakile farmakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel