An Rasa Rai 1, Sama da 100 Sun Jigata a Harin da Aka Kaiwa Tawagar Atiku, ‘Dan Takarar Gwamna a Borno

An Rasa Rai 1, Sama da 100 Sun Jigata a Harin da Aka Kaiwa Tawagar Atiku, ‘Dan Takarar Gwamna a Borno

  • Mohammed Jajari, ‘Dan takarar gwamnan jihar Borno a karkashin jam’iyyar PDP yace an halaka rai daya a farmakin da aka kai wa tawagar Atiku a Borno
  • Kamar yadda ya bayyana, a kalla sama da mutum 100 ne suka jigata inda wasu ke asibiti sun karbar taimako a Maiduguri babban birnin Borno
  • Jajari yace tun daga filin jirgin sama CJTF suka cire kayan aikinsu tare da mamaye tituna wanda yake zargin sune suka kai musu farmakin a wurin ralin

Borno - ‘Dan takarar kujerar gwamnan jihar Borno karkashin jam’iyyar PDP a jihar Borno, Mohammed Jajari, yace mutum daya ya rasa ransa yayin da sama da 100 suka jigata sakamakon harin da ‘yan daba suka kai kan tawagar kamfen din Atiku Abubakar.

Tawagar Atiku
Na Rasa Rai 1, Sama da 100 Sun Jigata a Harin da Aka Kaiwa Tawagar Atiku, ‘Dan Takarar Gwamna a Borno. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Atiku ya je Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Laraba domin yakin neman zabe yayin da lamarin ya faru, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

PDP ta tona sirri, ta fadi dalilin da yasa 'yan APC suka farmaki tawagar Atiku a Borno

Wadanda abun ya ritsa dasu an kai su asibitin jami’ar koyarwa ta Maiduguri inda suke karbar taimakon likitoci kamar yadda Jajari wanda ya bayyana a shirin gari ya waye na gidan talabijin na Channels TV a ranar Juma’a.

“Tun daga tasowar mu daga filin jirgi zuwa fadar Shehu, an zuba jami’an CJTF. Sun cire kayan aikinsu tare da badda kamanninsu kuma sun mamaye titunan har zuwa fadar.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- ‘Dan takarar gwamnan yace.

“Akwai duwatsu da sanduna da yawa ko a wurin ralin, an taimaka mutane masu yawa da suka samu rauni yayin da aka tura wasu asibitoci.
“Wurin ralin hankali kwance yake cike da lumana. Mun shigo kuma magoya bayanmu lafiya kalau muka samesu. Mun yi kamfen din mu hankali kwance amma mutanen da muka bari a titi sune muka sake bari yayin da zamu filin jirgin sama.”

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

- Ya kara da cewa.

Jajari ya tabbatar da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno ya ziyarci wurin kamfen din a ranar Laraba amma baya wurin yayin da suka fara kamfen din.

Kamar yadda ‘dan takarar kujerar gwamnan yace, barazanar da ‘yan jam’iyyar hamayya suka dinga wa PDP kafin kamfen din an sanar da hukumomin tsaro a matakin tarayya.

Ya zargi cewa yayin da bai san matakin da hukumomin tsaro suka dauka, jami’an tsaron dake tare da Atiku sun kama wasu da ake zargi.

“Rundunar ‘yan sandan jihar sun zo kuma suka dinga tambaya. Amma sun ce wadanda ake zargin zasu tafi dasu. Ban tabbatar ko sun yi hakan ba amma wasu daga cikinsu an kama su.”

- Jajari yace.

“Mun aike korafi zuwa Ofishin IGP, DSS, Ofishin mai bada shawara kan tsaron kasa, kuma dukka mun aike kwafi ga PDP reshen jihar. Mun yi hakan a makon da ya gabata tun kafin mu yi ralin. Amma abinda na sani shi ne babu matakin da aka dauka.”

- Jajari yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel