Kasuwar canji: Naira ta Bada Mamaki, Dala Tayi Mummunan Fadi, Ta Rasa Kusan N200

Kasuwar canji: Naira ta Bada Mamaki, Dala Tayi Mummunan Fadi, Ta Rasa Kusan N200

  • A karshe makon da ya gabata sai da masu Dalar Amurka suka saidawa jama’a $1 a kan N910 a Najeriya
  • Maganar da ake yi a yanzu kuwa, da N720 za ka iya sayen Dala, ana tunanin farashin zai kara sauka
  • Dala ta tashi sosai a makon nan bayan CBN ya bada sanarwar za a canza manyan takardun kudi a kasar nan

Nigeria - Naira ta samu gagarumar daraja a kan Dalar Amurka a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba 2022 bayan $1 ta kai kusan N885 a kasuwa.

Nairametrics tace a yammacin jiya, sai da aka saida Dala a kan N718 a kasuwa. Kafin nan kuwa sai mutum yana da kusan N815 zai iya mallakar Dala $1.

A cikin ‘yan awanni Naira ta tashi da 11.89% a karshen makon nan. Hakan na zuwa ne bayan jami’an EFCC sun dura kan masu cinikin kudin ketare.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Abubakar A Kotu Kan Satar Burodi A Kaduna

Masu harkar canjin kudi sun shaidawa jaridar cewa Dalar ta karye a karshe makon nan.

Farashi ya canza har a banki

A bankuna kuwa, farashin Dala ya koma N445.67/$1 daga ranar Larabar nan, hakan ya nuna Naira ta na tashi yayin da kudin kasar wajen ke rage daraja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Canjin farashin da aka samu a cikin ‘yan awanni a kasuwar canji ya kai 20.8% a sakamakon fadin Dala. Rahoton da Punch ta fitar ya tabbatar da haka.

Naira
Naira da Dalar Amurka Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Abin N910 ya zama N700+

A karshen makon jiya sai da masu canjin kudi suka saida Dala daya a kan N910, abin da masana tattalin arziki suka ce ba a taba jin labari a tarihin kasar ba.

Daga ranar Litinin dinnan aka ji jami’an EFCC sun tasa masu canjin kudi a manyan garuruwan Abuja, Legas, Kano da sauransu, hakan ya kawo sauki.

Kara karanta wannan

Ba Zai Yiwu A Cigaba Da Sayar Da Litan Man Fetur N170 ga Lita Ba, Shugaban NNPC

Hukumar EFCC ta cafke ma’aikatan Bureau De Change watau ‘yan canji fiye da 90 a Najeriya bisa zargin laifin boye kudi da sauran ayyuka na assha.

A farkon makon nan farashin Dala ya koma tsakanin N860 da N850. Daga nan kuma Naira ta shiga farfadowa a kasuwar canjin har ta kai N720 a jiya.

Mustafa Abdullahi, wani ‘dan canji a filin tashin jirgin saman Legas ya shaidawa Punch cewa a N715 ya saye Dala, kuma ya saidawa jama’a a kan N720.

Wani ‘dan canjin mai suna Sarki Muhammed, yace a N717 ya saye Dala, ya saida N721.

Kudi sun fara fitowa

A wani rahotonmu, kun ji an dauki bidiyon wasu ‘Yan N200 da aka buga tun a 2003, a lokacin ne Muhammadu Buhari ya shiga siyasa domin ya yi takara.

Saboda wasu dalilai, ana zargin Attajirai da jami'an gwamnati sun dankare kudi, sai da aka ji bankin CBN zai canza Naira sannan ake maida su banki.

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Cikin Makonni 2 Da Sanarwa, Jama'a Sun Kai Kudi N52bn Bankuna

Asali: Legit.ng

Online view pixel