Abuja: Yadda tsadar 'Pure water' ya sa mazauna birnin tarayya suka koma shan ruwan famfo

Abuja: Yadda tsadar 'Pure water' ya sa mazauna birnin tarayya suka koma shan ruwan famfo

  • Wasu mazauna babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana yadda su ka koma shan ruwan famfo bayan fiya wata ya yi tsada, inda ya koma ko wanne daya N20 maimakon N10
  • Sun bayyana hakan ne inda wasu suke zargin tashin farashin ya biyo bayan tsadar kayan aiki inda masu yin fiya watan su ka ga ba za su samu riba ba idan ba haka su ka yi ba
  • Wata mata ta zargi masu hada fiya watan da dura ruwan famfo a cikin leda ba tare da sarrafa shi ba kuma yanzu ba zai yuwu mutum ya ci gaba da tafasa ruwa ba saboda tashin sinadarin gas

FCT, Abuja - Wasu mazauna babban birnin tarayya, Abuja sun koma shan ruwan famfo maimakon fiya wata saboda tsadar rayuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso

A binciken da NAN ta gudanar ta gano cewa yanzu haka kudin fiya wata ya nunka kansa, don maimakon N10 ko wacce leda, yanzu ta koma N20.

Yadda tsadar 'Pure water' ya sa mazauna Abuja suka koma shan ruwan famfo.
Yadda tsadar 'Pure water' ya sanya mazauna Abuja suka koma shan ruwan famfo. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Mazauna yankin da su ka tattauna da NAN sun bayyana yadda a baya suke siyan fiya wata saboda yadda su ka yarda da ingancin sa fiye da na famfo.

Sai dai bayan tashin abubuwa a kasuwa, sun fara zargin akwai masu kamfanin ruwan da suke zuba ruwan famfo ba tare da tace shi ba su na sayar wa jama’a.

Wata Mrs Adams Yinka, ta sanar da NAN yadda yanzu rayuwa ta yi mu su kunci bayan kudin ruwa ya nunka kan sa inda ta ce:

“Yanzu mun dena siyan fiya wata tunda akwai wasu hanyoyin da ake bi don samun ruwa mai tsafta da lafiya.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 50: Tsohon sanata na tsare a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi

“Wasu kamfanonin da suke hada fiya watan ma basu da tsafta kuma yanzu wasu ma siyan injin matse leda suke yi su dinga zuba ruwa a leda su na rufewa haka nan.
“Duk da dai yanzu tafasa ruwa ma ya fi tsada shiyasa zai yuwu ruwan famfo ma suke amfani da shi, wasun mu sun koma amfani da ruwan gora.”

Wani mazaunin kubwa ya ce haka nan su ke siya

Wani mazaunin Kubwa da ke Abuja, Hamza Jimoh ya bayyana cewa:

“Tunda dole ne amfani da ruwa, wajibi ne siyan fiya wata duk da dai ya yi tsada yanzu.”

Ya kara da bayyana yadda har yanzu suke siyan ruwan duk da ya koma N20 saboda har yanzu tsadar shi ba ta yi yawa ba duk da dai ruwan gora ya fi kyau amma ya fi tsada.

Ya ce sakamakon tashin gas, yanzu tafasa ruwa ba ya yuwuwa saboda tashin gas, har gara mutum ya siya fiya wata kawai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel