Jami’an EFCC Sun Dura Jihar Jigawa, Sun Kame Tsohon Kwamishinan Gwamna Badaru

Jami’an EFCC Sun Dura Jihar Jigawa, Sun Kame Tsohon Kwamishinan Gwamna Badaru

  • Hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi ram da wani jigaon jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa
  • An kama Hon. Aminu Ahmed Kanta ne a jiya Litinin 7 ga watan Nuwamba, an tafi dashi birnin Abuja
  • Wata kotu ta ba da umarnin jami'an tsaro su kama shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa bisa zargin saba umarnin kotu

Jihar Jigawa - A karin kokarin aiki tukuru gabanin babban zaben 2023, hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC ta tura jami'anta jihar Jigawa, inda suka tsohon kwamishinan harkokin kananan hukumomi na jihar, Hon. Aminu Ahmed Kanta.

Kanta ya rike kujerar kwamishina a gwamnatin gwamna Badaru, kana ya rike kujerar mai ba da shawara ga gwamnan kan harkokin siyasa.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa, tsohon kwamishinan da aka kama ranar Linitin tuni aka taho dashi Abuja domin yi masa binciken kwa-kwaf.

EFCC ta kama na hannun daman gwamnan Jigawa
Jami’an EFCC Sun Dura Jihar Jigawa, Sun Kame Tsohon Kwamishinan Gwamna Badaru | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kanta, wanda kuma jigon siyasar APC ne kuma abokin siyasa ga Badari, yanzu haka shine dan takarar majalisar wakilai ta kasa a mazabar Garki/Badaru a zaben 2023 mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da cewa ba a bayyana dalilin kame shi ba, amma dai ba zai rasa nasaba da ofishin da ya rike da kuma wata dambarwar siyasa ta jihar Jigawa ba.

An ba da umarnin kama shugaban EFCC

Baya ga wannan, rahoto ya bayyana yadda kotu ta ba da umarnin kwamushe shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa.

An ruwaito cewa, alkalin kotun, Chizob Orji ya kama Abdulrasheed da laifin kin bin umarnin kotu.

Wannan umarni na kotu ya ce a 'yan sanda su kamo shi, kana su gaggauta kai magarkamar Kuje don zaman jira, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Babu batun cire Ajami a kudi, a kuma za a kirkirar N2,000, N5,000 da N10,000 ba

A wani labarin kuma kunji cewa, babban bankin Najeriya ya karyata jita-jitan kirkirar sabon kudin da ya haura N1,000 kamar yadda wasu jama'ar kasar ke yadawa.

Hakazalika, EFCC ya magantu kan batun cire rubutun Ajami a jikin kudaden da yake sauyawa fasalin nan da karshen wannan shekarar.

A bangare guda, bankin ya yi tsokaci tare da ba 'yan Najeriya shawarin yadda za su gane sabbin kudaden da ake bugawa don ci gaban kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel