An Raba N10m da Aisha Buhari Ta Bayar a Ba Mutum 200 da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Benue

An Raba N10m da Aisha Buhari Ta Bayar a Ba Mutum 200 da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Benue

  • Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta ba da tallafi ga jama'ar jihar Benue da ambaliyar ruwa ta shafa a daminin bana
  • Hukumar ba da agaji ta SEMA ta tabbatar da raba N10m tsakanin mutane 200 mazauna yankuna biyar a karamar hukumar Makurdi
  • Hukumar kula da yanayi ta gargadi 'yan Najeriya kan ambaliyar ruwa da za fuskanta a wasu watanni biyu na shekarar nan

Makurdi, Benue - Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Benue (SEMA) a ranar Talata ta tabbatar da ba da N10m da uwar gidan shugaban kasa Muhammadu ta bayar a rabawa mutane 200 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Idan baku manta ba, Aisha Buhari, ta hannun uwar gidan dan takarar shugaban kas ana APC, Sanata Oluermi Tinubu ta ba da kyautar N10m ga al’ummar jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Arewa yayin da 'yan bindiga suka sace wani Limamin Katolika

Hakazalika, rahoto ya bayyana cewa, ta ba da umarnin a yi gaskiya wajen raba kudaden ga mutane 200 da ambaliyar ruwa ta rutsa dasu a kewayen karamar hukumar Makurdi ta jihar.

Aisha Buhari ta ba da tallafi a Benue
An Raba N10m da Aisha Buhari Ta Bayar a Ba Mutum 200 da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Benue | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda aka yi rabon kayayyakin da kuma wadanda suka ci gajiyar rabon

Babban Sakateren SEMA a jihar, Dr Emmanuel Shior ya bayyana cewa, daidai da umarnin uwar gidan Buhari, an yi nasarar raba wadanda kudade ga wadanda suka dace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce an raba kudaden ne tabbas ga mutane 200 a yankuna biyar na Makurdi da suka fi shiga taskun ambaliyar ruwan daminan bana.

Wadanda suka ci gajiyar wanna gudunmawa sun yaba wa Aisha Buhari bisa wannan babban karimci, kamar yadda Daily Sun ta ruwaito.

Jihohi da dama a Najeriya sun fuskanci annobar ambaliyar ruwa, gidaje sun rushe, gonaki sun lalace, kasuwanni sun baci, hakazalika an yi asarar rayuka a daminan bana.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta dura Jigawa, ta kama wani babban na hannun daman gwamna

Kungiyoyi da dama sun yi kira ga samar da tallafi daga gwamnati, tuni kuma wasu ‘yan siyasa a kasar suka ba da gudunmawar rage radadin wannan ambaliya.

Gargadin hukumar kula da yanayi ta NiMet

A tun farko, hukumar kula da yanayi ta kasa NiMet ta gargadi 'yan Najeriya cewa, za a fuskanci matsanancin ambaliyar ruwa a watannin Agusta da Satumban bana.

Hakazalika, hukumar ta ba 'yan kasar shawarin yadda za su magance yaduwar ambaliyar ta hanyar kula da shara da magudanan ruwa a unguwanni.

Shugaban hukumar, Farfesa Mansur Bako Matazu, ya danganta samun ambaliyar ne da karuwar saukar ruwan sama da za a yi a watannin biyu, kamar yadda ya fadi a tattaunawarsa da Channels Tv.

Asali: Legit.ng

Online view pixel