Nasara daga Allah: An Halaka Yan Bindiga Sama da 50 a Jihar Neja

Nasara daga Allah: An Halaka Yan Bindiga Sama da 50 a Jihar Neja

  • Haɗin guiwar jami'an tsaro sun samu gagarumar nasarar sheƙe 'yan ta'adda sama da 50 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro, jihar Neja
  • Wasu bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun kai hari wata ruga, bayan samun rahoton jami'an tsaron suka tarbe su aka fafata
  • Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida da ayyukan jin kai na jihar Neja, Mista Umar, ya tabbatar da kai harin

Niger - 'Yan ta'adda sama da 50 ne suka baƙunci Lahira a kauyen Chibani, ƙaramar hukumar Shiroro, jihar Neja yayin musayar wuta da gamayyar jami'an tsaro.

Jaridar The Nation tace 'yan ta'addan sun mamayi wata Rugar Fulani a yankin Chibani, suka yi awon gaba da Shanu sama da 200 lokacin da mazauna Rugar ke shirye-shiryen tashi saboda zuwan lokacin rani.

Taswirar jihar Neja.
Nasara daga Allah: An Halaka Yan Bindiga Sama da 50 a Jihar Neja Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

Sa'ilin da maharan suka kai harin, mutane sun yi gaggawar sanar da haɗakar jami'an tsaron waɗanda suka bi sawun yan ta'addan aka fara musayar wuta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Bude Wuta Kan Mutane a Shingen 'Yan Sanda, Rayuka Sun Salwanta

An rahoto cewa 'yan Banga biyu ne suka rasa rayuwarsu sanadin Artabun yayin da 'yan ta'adda da yawa suka taere da muggan raunuka a jikkunansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyukan jin ƙai na jihar Neja, Emmanuel Umar, ya tabbatar da kai harin, yace tuni aka tura dakarun tsaro domin kai ɗauki.

Sai dai ya ƙi cewa uffan game da rayukan da aka rasa daga kowane ɓangare, inda yace, "Har yanzun ana kan aiki kan batun."

Jihar Neja na ɗaya daga cikin jihohin arewa ta tsakiya a Najeriya da ke fama da ayyukan ta'addancin 'yan bindiga, waɗanda hukumomi a Najeriya suka ayyana su a matsayin 'yan ta'adda.

A 'yan watannin nan hukumomin tsaro a Najeriya sun ce suna samun galaba kan masu ta da ƙayar baya, duk da ana samun rahoton kai hare-hare jefi-jefi a wasu sassan ƙasar.

Kara karanta wannan

Mutuwa Rigar Kowa: Mutane Sama da 12 Sun Kone Kurmus a Jihar Kano

Ana Fargabar Da Yawa Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Bude Wuta a Shingen Yan Sanda

A wani labarin kuma wasu tsageru sun kai kazamin hari kan mutane a wani Shingen bincike na yan sanda a jihar Anambra

Mutane sun shiga tashin hankali sanadin harin kuma ana tsammanin mutane da dama sun rasa rayukansu.

Bayanai sun nuan ceqa jami'an tsaron da ke aiki a wurin sun cire kakin aikinsu, kana sun ɗauki matsaya an cigaba da musayar wuta da maharan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel