Mutum 14 Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsari da Ya Auku a Kano

Mutum 14 Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsari da Ya Auku a Kano

  • Aƙalla Fasinjoji 14 ne suka rasa rayukasu yayin da wata Motar Kano Line ta yi taho mu gama da Jeef a titin Gaya-Wudil, jihar Kano
  • Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra reshen Kano, Zubairu Mato, ya tabbatar da yawan mutanen da aka rasa sanadiyyar hatsarin
  • Ya yi kira ga direbobi su riƙa amfani da na'urar kula da yawan gudu kuma su guje wa tsere a kan manyan Tituna

Kano - Hukumar kiyaye haɗurra ta tabbatar da mutuwar Fasinjoji 14 waɗanda suka ƙone a kan Titin Gaya zuwa Wudil, jihar Ƙano sakamakon hatsarin Motar Bas Toyota Hummer da Hyundai jeep.

Kwamandan hukumar reshen jihar Kano, Zubairu Mato, shi ne ya tabbatar da alƙaluman waɗanda suka rasu ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Taswirar jihar Kano.
Mutum 14 Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsari da Ya Auku a Kano Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Yace jami'an hukumar FRSC sun kai ɗauki wurin da haɗarin ya faru a ƙauyen Rage dake Titin Kano-Gaya da misalin ƙarfe 7:45 na dare.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan Bindiga Sama da 50 Sun Bakunci Lahira a Jihar Arewa

Kwamandan ya yi bayanin cewa Motar Bas ɗin mai lambar Rijista GML 102 TA mallakin kamfanin Sufurin Kano Line ta taso ne daga Gombe lokacin da ta yi taho mu gama da Motar Jeep da ƙarfe 7:30 na daren Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace, "Fasinjoji 13 suka ƙone har Lahira nan take yayin da wasu mutum Shida suka ji raunuka aka nufi Asibiti da su."

An gano cewa ɗaya daga cikin Fasinjoji mata da Hatsarin da rutsa da ta rasu ranar Litinin da safe a Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Menene ya haddasa hatsarin?

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra, (FRSC), Zubairo Mato, ya alaƙanta abinda ya jawo hatsarin da gudun da ya wuce ƙima da kuma haɗarin tseren wuce na gaba, kamar yadda Tribune ta tattaro.

Bisa haka ya roki Direbobin mota su tabbata suna amfani da na'urar tantance gudu kuma su guje wa jefa rayukan mutane a haɗari wurin wuce na gaba a manyan Tituna.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa a APC, Wani Babban Jigo da Wasu Shugabanni Sun Ayyana Goyom Baya Ga Ɗan Takarar PDP a 2023

A wani labarin kuma wani ibtila'in Gobara ta yi ɓarna mai yawa a wata makarantar Tsangaya a jihar Kano

An ce Gobarar ta lalata ɗakunan kwana aƙalla 14 a makarantar mai suna Tsangaya Boarding Primary School dake ƙauyen Kanwa a ƙaramar hukumar Madobi.

Hukumar ba da gaji (SEMA) a madadin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kai ziyarar jaje makarantar tare da ba da tallafin rage raɗaɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel