Mummunan Hatsarin Mota Ya Lakume Rayukan Mutane 5 A Wata Jahar Arewa

Mummunan Hatsarin Mota Ya Lakume Rayukan Mutane 5 A Wata Jahar Arewa

  • Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar rasa ran wasu bayin Allah su biyar a jihar Bauchi
  • Hatsarin ya afku ne a a kauyen Isma da ke babban titin Bauchi zuwa Jos tsakanin motar Peugeot 406 da wata tankar DAF
  • Da yake tabbatar da lamarin, kwamandan hukumar FRSC jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce hatsarin ya wakana ne sakamakon mugun gudu da motocin suka kwaso

Bauchi - Wani mummunan al’amari ya afku a ranar Asabar yayin da mutane biyar suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota a kauyen Isma da ke babban titin Bauchi zuwa Jos.

Kwamandan hukumar kare afkuwar hadarurruka a jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da adadin wadanda suka mutun yayin da ya zanta da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Bauchi.

Jahar Bauchi
Mummunan Hatsarin Mota Ya Lakume Rayukan Mutane 5 A Wata Jahar Arewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa wasu mutum biyu sun ji mummunan rauni a hatsarin wanda ya afku tsakanin motar Peugeot 406 da wata tankar DAF.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ayu, Tambuwal da Sule Lamido Sun Gana Da Gwamnan Bauchi

Abdullahi ya alakanta faruwar hatsarin da gudu ba bisa ka’ida ba, rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Mummunan hatsarin ya cika da mutane bakwai, kuma sun hada da maza uku da mata uku sai yarinya karama daya.
“Maza biyu, mata biyu da karamar yarinyar sun mutu a nan take.
“Sauran biyun sun ji mummunan rauni.”

Mallam Abdullahi ya ce an dauki gawarwakin mamatan zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, rahoton PM News.

Ya koka kan rayukan da aka rasa sannan ya shawarci masu tuka mota da su dunga lura da bin ka’idojin tuki.

Mummunar Gobara Ta Yi Ajalin Bayin Allah Sama da 10 a Kano

A wani labarin, mun ji cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da kayayyaki da ya kai kimanin naira miliyan 20 suka salwanta sakamakon tashin gobara a wurare daban-daban a jihar cikin watan Oktoba.

Kara karanta wannan

2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi

Hakan na kushe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobarar, Alhaji Saminu Abdullahi, wanda aka fitar a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba, a garin Kano, PM News ta rahoto.

Abdullahi ya ce hukumar ta kuma kare rayuka 24 da dukiyoyi na kimanin miliyan N43.3 daga gobara 35 da suka tashi a wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel