Mummunar Gobara Ta Yi Ajalin Bayin Allah Sama da 10 a Kano

Mummunar Gobara Ta Yi Ajalin Bayin Allah Sama da 10 a Kano

  • Mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da kayayyaki na miliyoyin nairori suka salwanta sakamakon gobara da ta barke a wurare daban-daban a jihar Kano
  • Saminu Abdullahi, mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Kano, ya ce wannan al'amari ya afku ne a cikin watan Oktoba
  • Abdullahi ya ce sun ceto mutum 24 da dukiya kimanin miliyan N43.3 daga tashin gobara 35 a watan da ya gabata

Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da kayayyaki da ya kai kimanin naira miliyan 20 suka salwanta sakamakon tashin gobara a wurare daban-daban a jihar cikin watan Oktoba.

Hakan na kushe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobarar, Alhaji Saminu Abdullahi, wanda aka fitar a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba, a garin Kano, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Alkali Ya Aike ‘Yan TikTok 2 Kurkuku Kan Zagin Ganduje da Bata Masa Suna

Jihar Kano
Mummunar Gobara Ta Yi Ajalin Bayin Allah Sama da 10 a Kano Hoto: Punch
Asali: UGC

Abdullahi ya ce hukumar ta kuma kare rayuka 24 da dukiyoyi na kimanin miliyan N43.3 daga gobara 35 da suka tashi a wannan lokaci.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta amsa kiraye-kirayen ceto 32 da kuma na karya guda shida daga al’umma a fadin jihar a tsakanin lokacin da ake magana a kai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin hukumar ya bukaci jama’a da su lura sosai kan yadda suke aiki da wuta don gudun sake afkuwar irin haka a gaba.

Ya kuma gargadi masu ababen hawa da su dunga bin dokar tuki a hanya don hana afkuwar hatsarurruka a jihar, rahoton Pulse.ng.

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani gini mai hawa ɗaya ya rufta a ranar Juma'a, ya yi sanadin rasuwar yaya da kani masu shekaru 15 da 11. Babban yayansu mai shekaru 17, shi an yi nasarar ceto shi da ransa, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na Jihar Kano, Saminu Abdullahi, a ranar Asabar ya ce gidan da abin ya faru yana unguwar Kofar Mata, Hauren Gadagi a Kano.

Mr Abdullahi ya kara da cewa an garzaya da wadanda abin ya faru da su zuwa Asibitin Murtala Muhammad don likitoci su duba su idan aka tabbatar biyu cikinsu sun rasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel