'Ku Agaza Mana': Iyaye Sun Koka Yayin da Yan Bindiga Suka Sace Kananan Yara Sama da 30 a Jihar Buhari

'Ku Agaza Mana': Iyaye Sun Koka Yayin da Yan Bindiga Suka Sace Kananan Yara Sama da 30 a Jihar Buhari

  • Tsagerun yan bindiga sun kai farmaki wata gona a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina inda suka yi awon gaba da yara 39
  • Iyayen yaran sun koka yayin da suka roki gwamnati da ta taimaka ta kubutar masu yaransu domin harda mata da suka isa aure a ciki
  • Yan bindigar sun farmakin gonar ne da nufin sace mai gonar da wakilinsa amma sai suka tarar basa nan don haka suka kwashe yaran

Katsina - Iyaye a garuruwan karamar hukumar Faskari, inda yan bindiga suka sace yara 39 yayin da suke tsaka da aiki a gona sun roki gwamnati da ta ceto yaran daga hannun wadanda suka sace su.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigar sun mamaye wata gona a ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da yara fiye da 40 da suka hada da maza da mata yayin da suke tsaka da aiki.

Kara karanta wannan

Niger: ‘Yan Ta’adda Sun Halaka Mafarauta 5, Sun Yi Garkuwa da Fasinjoji Babu Adadi

Wata majiya a garin Mairuwa, inda harin yafi muni ta ce yan bindigar sun mamaye gonar sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi kafin suka sace ma'aikatan.

Yan bindiga
Iyaye Sun Koka Bayan Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Yara 39 Daga Gona A Wata Jahar Arewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce wakilin mai gonar ya tara yaran bayan ya biya yan bindigar harajin naira miliyan 1, inda ya kara da cewar yawancin manyan da ke aiki a gonar sun yi nasarar tserewa a yayin harin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sun bukaci naira miliyan 3 daga mai gonar kafin ya iya girbe amfanin gonarsa, ya basu naira miliyan 1 don rage hanya sannan ya yanke shawarar fara aiki kafin ya cika sauran kudin, amma abun bakin ciki yan bindigar basu yarda da hakan ba. A kauyenmu, Mairuwa kadai muna da mutum 33 cikin wadanda aka sace harda yan mata da suka isa aure," in ji majiyar.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Wani mazaunin garin Mairuwa wanda ya tabbatar da wannan labari ya ce:

"Mai gonar dan Funtua ne, amma wakilinsa na zama a nan kauyen Mairuwa. Yanzu da mike magana, yan bindigar sun yi amfani da wayar daya daga cikin mutanen da abun ya ritsa da su inda suka bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 30.
"Sun ce sun farmaki gonar ne don sace mai gonar ko wakilinsa amma saboda basu samu kowannensu ba sai suka yanke shawarar garkuwa da wadanda ke masu aiki."

Daily Trust ta tattaro cewa gidan wakilin mai gonar na cike da iyayen wadanda aka sace a ranar Litinin inda suka ta kokawa kan mummunan lamarin, inda wasu suka zarge shi da jefa rayukan yaransu a cikin hatsari.

Lamarin ya sa yan sanda sun tsare mutumin kafin aka bayar da belinsa daga baya.

An kuma tattaro cewa garuruwa da dama a karamar hukumar na ciki radadi domin sai sun biya yan bindigar miliyoyi kafin su iya girbe amfanin gonarsu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Fashewar Janareto Ya Haddasa Mummunar Gobara a Legas

Wani mazaunin Katoge a karamar hukumar Kankara ya bayyana cewa yan bindigar sun sanya harajin naira miliyan 2 kan kauyensa kafin su iya aiki a gonakinsu amma daga baya suka sasanta kan N600,000.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce ana kokarin ganin an ceto mutanen tare da hadin gwiwa tsakanin yan sanda, gwamnatin jihar da sauran hukumomin tsaro.

An rahoto cewa shida daga cikin mutanen sun samu yanci a ranar Talata.

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutum `10 A Zamfara, Sun Bukaci A Biya N20m Kudin Fansa

A wani labarin, yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 10 a wasu garuruwa biyu da ke kauyukan Dogondaji da Kazauda a yakin Wanke, karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Maharan sun kuma bukaci a biya naira miliyan 20 a matsayin kudin fansar mutanen.

A hira da yayi da jaridar Punch ta wayar tarho, wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Musa ya ce mutum shida aka sace a kauyensa na Kazauda yayin da aka sace hudu a kauyen Dogondaji inda suka bukaci naira miliyan 2 kan kowanne.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Halaka Mahaifin Budurwarsa Mai Shekaru 68 a Bauchi

Asali: Legit.ng

Online view pixel