Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

  • Bashir Magashi ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da ganin cewa hukumomin tsaro sun fara samun jawabin gargadi daga kasashen waje kafin su isa ga jama’a
  • Ministan tsaron ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai
  • An dai shiga halin fargaba a kasar a baya-bayan nan sakamakon gargadin da kasashen US da UK suka yin a yuwuwar kai hari a Abuja

Abuja - Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya ce addu'a Najeriya ke bukata daga gwamnatin Amurka maimakon gargaji wanda ya jefa mutane cikin rudani.

Ministan ya bayyana cewa gargadin da Amurka tayi kan yuwuwar kai harin ta'addanci a Abuja ya jefa jama'a cikin tsoro sannan ya razanar da yan Najeriya ta yadda har sun gaza daukar matakin da ya dace, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Fashewar Janareto Ya Haddasa Mummunar Gobara a Legas

Sai dai kuma, ya bayyana cewa barazanar bai yi tsanani ba, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnati na kan lamarin da taimakon hukumomin tsaro da na leken asiri.

Magashi
Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

Magashi ya yi magana ne yayin da yake kare kasafin kudin ma'aikatar tsaro na 2023 a gaban kwamitin majalisar wakilai, rahoton The Cable.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabinsa martani ne kai tsaye ga wata tambaya da shugaban kwamitin majalisar, Hon. Babajimi Banson yayi kan abun da yake yi don magance gargadin da wasu kasashen waje ciki harda Amurka suka yi kan tsaro.

Magashi ya ce:

"Idan kun tuna, a jiya kwamitin tsaro sun gana sannan mun tattauna wannan barazanar kuma mun yarda cewa ba abu ne da zamu yiwa rikon sakainar kashi ba. Mun yi kokarin tabbatar fa tushen barazanar ko jawabin da gwamnatin Amurka tayi. Mun yi kokarin gano kasashen da ke da ra'ayi a jawabin da gwamnatin Amurka tayi kuma mun ga cewa hanya mafi dacewa da za a bi da lamarin shine ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Abuja da jihohin da ke makwabtaka, wato Nasarawa, Neja da sauransu.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

"Sai dai kuma, mun yarda cewa ruwa baya tsami banza kuma dangane da hakan, mun yi nasarar gabatar da lamarin ga hukumomin leken asirinmu kuma sun gabatar da amsoshi a wuraren da gwamnati ke shakku kuma mun gano cewa muna bukatar sanya idanu sosai don hana duk wasu ayyukan yan bindiga, wanda daga nan ne barazanar zai iya faruwa, za mu samar da isassun runduna da za su iya kawar da irin wadannan lamuran.
"Ina mai ba mambobin majalisa tabbacin cewa gwamnati na kan lamarin. Bisa ga taron tsaro da abun da muke da su a kasa, ina ganin abun da muke bukata daga Amurka addu'a ce ba wai bamu bayanan da zai jefa al'ummarmu a rudani ko rashin daukar matakin da ya dace. Kuma ministanmu na harkokin waje zai dauki mataki kan wannan don ganin cewa an gabatar bayani irin haka a gaban ma'aikatar kafin watsa shi cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da Gwamna El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni hudu saboda wani dalili

"Ina ganin muna kan lamarin. Barazanar bai yi tsanani ba kuma muna daukar mataki. Muna yin duk wanda zamu iya don tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a Najeriya.

Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa da Hafsoshin Tsaron Kasa a Abuja

A gefe guda, mun ji a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro na kasa a kan lamarin tsaro.

Kamar yadda mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwar zamani, Buhari Sallau ya sanar a shafinsa na Facebook, taron na gudana ne a safiyar yau Litinin, 31 ga watan Oktoba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ana sanya ran za su sake bita da kuma karfafa lamarin tsaro a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel