Niger: ‘Yan Ta’adda Sun Halaka Mafarauta 5, Sun Yi Garkuwa da Fasinjoji Babu Adadi

Niger: ‘Yan Ta’adda Sun Halaka Mafarauta 5, Sun Yi Garkuwa da Fasinjoji Babu Adadi

  • Yan ta’addan sun kwashe fasinjoji da ba a san adadinsu ba yayin da suka rufe hanyar Garin Gabas dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja
  • Majiyoyi dake yankin sun ce matafiyan suna kan hanyarsu ta zuwa Kontagora ne yayin da ibtila’in ya fada kansu da yammacin Talata
  • Har ila yau, ‘yan ta’addan sun halaka mafarauta 5 da suka je kai wa matafiyan taimako inda wasu biyar suka jigata sakamakon fin karfinsu da aka yi

Niger - Matafiya masu tarin yawa da ba a san adadinsu ba har yanzu da suka nufi Kontagora an yi garkuwa da su yayin da ‘yan ta’adda suka halaka mafarauta biyar a kusa da Garin Gabas dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

‘Yan bindiga
Niger: ‘Yan Ta’adda Sun Halaka Mafarauta 5, Sun Yi Garkuwa da Fasinjoji Babu Adadi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, ‘yan ta’addan sun bayyana a sama da babura 40 inda suka rufe titin tare da tsayar da masu ababen hawa.

Kara karanta wannan

Borno: Sojin Najeriya Sun Halaka Sama da ‘Yan Ta’adda 15, An Rasa Sojoji 2

An gano cewa, farmakin ya faru tsakanin karfe 4 zuwa 5 na yammacin Talata.

Majiyoyi daga yankin sun ce har yanzu ba a san yawan fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba saboda kusan ababen hawa biyar ne aka kwashe fasinjojin dake ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyin sun ce mafarautan sun amsa kiran gaggawa da aka yi musu ne amma sai ‘yan ta’addan suka ci galaba a kansu inda suka raunata wasu biyar duk a harin.

Duk kokarin ji daga bakin jami’an tsaro da aka yi bai yuwu ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Niger, DSP Abiodun Wasiu ba ya gari inda ya tafi halartar wani muhimmin taro na manyan jami’an ‘yan sanda a Owerri amma yayi alkawarin karin haske idan ya samu bayanai kan farmakin.

Katsina: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari, Sun Sace Matafiya Da Dama

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Fashewar Janareto Ya Haddasa Mummunar Gobara a Legas

A wani labari na daban, an rahoto cewa wasu yan bindiga sun tare hanyar Katsina zuwa Jibia a ranar Laraba kuma suka sace matafiya da a yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Wani shaidan gani da ido ya ce harin ya faru ne misalin karfe 5 na yammacin kauyen Kadobe, Daily Trust ta rahoto.

Majiyar ta ce yan bindigan da suka taho kan babura shida, sun mamaye hanyar suka rika harbe-harbe don firgita matafiya sannan suka sace mutanen da ke cikin wasu motocci biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel