Da Duminsa: Fashewar Janareto Ya Haddasa Mummunar Gobara a Legas

Da Duminsa: Fashewar Janareto Ya Haddasa Mummunar Gobara a Legas

  • Wani gini ya kama da wuta sakamakon bindigar da janareto yayi a safiyar Talata a Victoria Island dake jihar Legas
  • Kamar yadda ganau suka sanar, wutar da ke cin ginin ta shafi wani gini dake farfajiyar tare da hadaw da wasu ababen hawa
  • Nosa Okunbor, mai magana da yawun LASEMA, ya tabbatar da cewa jami’anta na wurin kuma suna kokarin kashe gobara da bayar da agajin gaggawa

Victoria Island, Legas - Wani gini dake Adeola Odeku a Victoria Island dake jihar Legas a halin yanzu yana nan yana ci da wuta.

Legas
Da Duminsa: Fashewar Janareto Ya Haddasa Mummunar Gobara a Legas. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

An gano cewa gobarar ta tashi ne sakamakon bindiga da janareto yayi wanda ya aiki a sa’o’in farko na ranar Talata, jaridar TheCable ta rahoto.

Kamar yadda ganau suka bayyana, wata mota dauke da fasinjoji uku da ta tsaya kusa da ginin da ya kama da wuta duk sun kurmushe.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tashin gobarar ya shafa wasu ababen hawa tare da wani gini dake farfajiyar.

A yayin tabbatar da faruwar lamarin, Nosa Okubor, mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa, LASEMA na jihar, yace jami’an hukumar a halin yanzu suna inda abun ke faruwa.

Yace Hukumar na lura da abinda ke faruwa inda ya kara da cewa tawagar agajin gaggawa suna aiki don kwantar da ibtila’in.

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, wutar ta lamushe rayukan mutum tara bayan wani banki da ake ginawa ya kama da wuta.

LASEMA ta tabbatar da cewa an rasa mutum tara dukkansu maza ne kuma manya. Sun samu miyagun raunika da kuna kuma an kai su asibiti.

“Bincike da aka tattaro daga wurin da abun ya faru ya tabbatar da cewa janareto ne ya tada ta.”

- LASEMA tace.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An Hana Jirage Tashi Yayin da Ma’aikata Suka Rufe Inda Jirage Suke a Legas

Wata mota mallakin rundunar RRS ta kurmushe yayin da take farfajiyar ginin.

Gobara ta tashi Babban Asibitin Asokoro a Abuja

A wani labari na daban, wani sashi na babban asibitin yankin Asokoro da ke birnin tarayya Abuja ya kama da wuta, rahoton The Punch.

Ba bu tabbas ko an rasa rai sakamakon gobarar.

Channels Television ta rahoto cewa daga bisani an yi nasarar kashe wutan.

Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, cikin wani sako da ta wallafa a Twitter ta ce:

"Jami'an mu sun yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a Babban Asibitin Asokoro a Abuja."

Asali: Legit.ng

Online view pixel