Kotun Musulunci a Kaduna Ta Raba Sabon Aure Na Wata Daya Kan Abu Daya

Kotun Musulunci a Kaduna Ta Raba Sabon Aure Na Wata Daya Kan Abu Daya

  • Kotun Shari'a ta raba wani sabon aure da bai wuce wata ɗaya ba sakamakon matar ta amince da biyan sadakin 100,000
  • Bayanai sun nuna cewa Amaryar, Maryam Dahiru, ta shigar da kara gaban Kotun, tana neman Saki daga Mijinta ta hanyar Khul'i
  • Magidancin ya nuna bai shirya sakin matarsa ba saboda yana sonta amma ya nemi ta maida masa da Akwatunan da ya yi

Kaduna - Kotun Shari'ar Musulunci dake zama a Magajin Gari, Kaduna, a ranar Litinin ta umarci wata matar aure, Maryam Ɗahiru, ta dawo da sadakin N100,000 da kayan akwatin da ta karɓa daga tsohon mijinta, Salihu Yakubu.

Da yake yanke hukunci, Alƙalin Kotun mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, ya tabbatar da raba auren tsakanin mutanen biyu ta hanyar Khul'i (Wato yarjejeniyar saki ta fahimta).

Kotun Shari'a a Kaduna.
Kotun Musulunci a Kaduna Ta Raba Sabon Aure Na Wata Daya Kan Abu Daya Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto Alkalin na cewa:

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari

"Zata dawo da kayan da bata taɓa sanya wa ba kaɗai kuma ita da ta kawo ƙara tana da umarnin Kotu ta koma ta kwashe kayanta daga gidan tsohon mijinta."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meya jawo raba auren na wata ɗaya?

Tun farko dai, Maryam ta hannun Lauyanta Murtala Gyallesu ta shigar da ƙarar mijinta ranar 12 ga watan Oktoba, 2022 tana mai rokon Kotu ta rabasu ta hanyar Khul'i.

Ta shaida wa Kotun cewa bata sha'awar ci gaba da zaman auren kuma a shirye take ta biya kudin sadaƙin da aka biya a kanta domin samun takardar saki.

A na shi ɓangaren Salihu Yakubu ta bakin lauyansa M. M. Ɗahiru, ya faɗa wa Alkalin cewa har yanzun yana ƙaunar matarsa kuma bashi da niyyar sakinta.

Ya kuma roki Kotun ta umarci tsohuwar matarsa ta dawo masa da akwatunan da ya cika da kayayyaki, wanda ya bata a matsayin kyauta lokacin aurensu.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Magidanci a Yobe da Garkame Matarsa Tsawon Shekara 1, Baya Bata Abinci Sai Koko

A wani labarin kuma Wata Hamshakiyar Mai Kudi a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m

Wata Mai kuɗi dake zaune a Birnin tarayya Abuja ta shiga neman kyakkyawan Saurayin da zai iya ɗirka mata ciki.

Attajirar ta yi alkawari baiwa duk wanda iya wannan aiki kuɗi naira Miliyan Uku amma akwai sharuddan da ta kafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel