Zankadediyar Budurwa Tace Masu Kudi Sun Cika Girman Kai, Ta Neman Saurayi Mara Ko Sisi

Zankadediyar Budurwa Tace Masu Kudi Sun Cika Girman Kai, Ta Neman Saurayi Mara Ko Sisi

  • Wata kyakkyawar budurwa ajin farko ta bayyana irin saurayin da take muradin samu wanda ya ba mutane mamaki
  • A cewar shafinta na Twitter, masu kuɗi sun cika jiji da kai kuma a yanzun tana fatan haɗa alaƙa da Talaka mara ko sisi
  • Yayin da wasu suka yi mamakin kalaman budurwar, Samarin da suka lashe yawu ba su bata lokaci ba wajen kokarin gwada sa'arsu

Wata zankaɗeɗiyar mace yar ƙasar Afirka ta kudu ta kuntata wa da yawan mutane da suka nuna sha'awa a kanta bayan ta bayyana wa duniya a Soshiyar Midiya cewa ta gama da mutane masu arziki.

A shafinta da dandalin Tuwita, @Ma_Dlamini_ budurwar ta saki kyawawan Hotunanta waɗanda ta sha kwalliya masha Allah ga gashinta mai kyau tare da yin rubutun da ya ja hankali.

Kara karanta wannan

Bidiyon Saurayi Ya Kaiwa Budurwa Ziyara a Kauye, Yayi Mata Wanki da Diban Ruwa

Kayakkyawar budurwa.
Zankadediyar Budurwa Tace Masu Kudi Sun Cika Girman Kai, Ta Neman Saurayi Mara Ko Sisi Hoto: @Ma_dlamini
Asali: Twitter

Ta rubuta cewa:

"Ina son samun Saurayi mara ko sisi. Masu kudi sun cika girman kai."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa la'akari da zamani da irin mutanen da mata ke fatan samu a yanzun, irin saurayin da matashiyar budurwa ta nuna ta na so ya baiwa da yawan mutane mamaki a Online.

Amma ta wani bangaren wannan wata babbar dama ce ga waɗanda ke kaunarta amma ba su da damar haɗuwa da ita.

Yadda mutane suka bayyana ra'ayoyinsu

@Pplembede ya rubuta cewa:

"Me zaki da mutumin da ba shi da ko sisi? Yayin da kyaunki ya kai haka."

@DanMakhoana yace:

"Ni dai ina tsaka tsakiya ne tsakanin Talauci da Arziki, ko hakan zai yi aiki."

@SphepheloZuma01 yace:

"Ni talaka ne sosai yar uwa kuma ina zaune ne a eNanda, zan iya."

@Sir_iBuyerSA ya rubuta ra'ayinsa da cewa:

"Ki nemi mutum mai fatan nasara, ki zame masa farin ciki kuma ƙashin samun arzikinsa, ba zai wulaƙanta ki ba zai kula dake tamkar sarauniya. Ni kaina na yi rashi ina fatan samun kyakkyawar gimbiya."

Kara karanta wannan

Wani Mutumi Ya Kaɗu Bayan Ya Laɓe Ya Ji Tattaunawar Matarsa da Kawarta a Waya, Bidiyo Ya Ja Hankali

A wani labarin kuma Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan yaduwar bidiyon wata kyakyyawar budurwa da ta kasa auruwa.

Budurwar wacce ta bayyana cewa za ta cika shekaru 39 a bana tace har yanzu bata samu wani tsayayyen namiji ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel