Bidiyon Saurayi Ya Kaiwa Budurwa Ziyara a Kauye, Yayi Mata Wanki da Diban Ruwa

Bidiyon Saurayi Ya Kaiwa Budurwa Ziyara a Kauye, Yayi Mata Wanki da Diban Ruwa

  • Bidiyon wani mutum yana wanki da wasu ayyukan na budurwar shi a kauye ya janyo cece-kuce a yanar gizo
  • Budurwar ta bayyanawa jama’a a bidiyo yayin da take bada labari dalla-dalla yanda ya nuna mata tsabar kauna
  • Baya ga wankinta, masoyinta ya taimaka mata wurin yin fenti tare da diban ruwa duk don ya farantawa matarsa

Wata budurwa ta dinga farin ciki da mijinta a soshiyal midiya kan yadda yayi mata ayyukan kauye kuma ta bayyana bidiyon domin nuna hazakarsa.

Budurwa da Saurayi
Bidiyon Saurayi Ya Kaiwa Budurwa Ziyara a Kauye, Yayi Mata Wanki da Diban Ruwa. Hoto daga TikTok/Lomberrym
Asali: UGC

Budurwar cike da murna tace ya ziyarceta a kauye kuma ya nuna mata kauna ba tare da bude baki ya furta mata ba.

A bidiyon da ta wallafa a TikTok, ta bayyana kayayyakin abinci da na bukata da ya kawo mata a kauyen.

Masoyinta ya kara da yi mata fentin dakinta tare da yi mata wanki har da girki. Ta kara da bayyana inda ya debo mata ruwa da daddare.

Kara karanta wannan

A Raba Ni Da Matata Kafin Hawan Jini Yayi Ajalina, Magidanci ga Alkali

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tace sau da yawa yana zazzagaya gari da ita yayin da yake rike da hannunta kuma yana mata kallon soyayya.

Har ila yau, saurayinta ya siya mata layin waya, wanda hakan ya matukar birgeta.

Yan soshiyal midiya sun yi martani

Pamela Ngoma Qu’abe tace:

“Chalilo na san wannan yankin amma nan taba ziyartarsa ba, ina aiki a mukando. Wata rana zamu iya haduwa.”

Abrahamchilubaila yace:

“Me kika bai wa wannan matashin da yake Haka?”

User713938354248:

“Wannan abu yayi kyau. Ku dinga yi wa juna addu’a kuma Ubangiji ya kare alakarku.”

nchimunya912 yace:

“Kai wannan abu yayi kyau. Ina ma Ubangiji zai saka muku albarka.”

Shebbymemory yace:

“Wannan abu yayi kyau, Allah ya kasance da ku ta yadda zaku yi rayuwa tare cikin kauna.”

Bidiyon Budurwa da ta Kone Kwalin Digirinta Bayan Shekaru 4 Tana Neman Aiki

Kara karanta wannan

Yadda Wani Mutum Ya Makance Bayan Ya Auri Makauniya Da Mijinta Ya Tsere Ya Bar Ta, Sun Bada Labarin Soyayyarsu

A wani labari na daban, Bridget Thapwile Soko, budurwa ‘yar kasar Malawi wacce tayi digiri a fannin kasuwanci ta fito bainar jama’a ta bankawa shaidar digirinta wuta.

Ta matukar fusata ne saboda shekaru hudu da ta kwashe da kammala karatu amma bata samu aiki ba.

A bidiyon kai tsaye da tayi a TikTok, matashiyar budurwar ta rera waka tare da zunden duk wanda ya gaza bata aiki ko kuma ya ki gayyatarta tantancewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel