Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan yaduwar bidiyon wata kyakyyawar budurwa da ta kasa auruwa
  • Budurwar wacce ta bayyana cewa za ta cika shekaru 39 a bana tace har yanzu bata samu wani tsayayyen namiji ba
  • Da take bayyana lamarinta a matsayin mara tabbass, ta roki Allah da ya kawo mata doki tare da share mata hawayenta

Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.

Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.

Budurwa
Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo Hoto: TikTok/@pwincex_mimi
Asali: UGC

Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.

Kara karanta wannan

Hatta Mijina Yana Alfahari dani: Mahaifiyar Yara 2 Direban Tasi Ta Birge Jama’a a Bidiyo

Ta bayyana lamarinta a matsayin mara tabassa sannan ta roki Ubangiji da ya kawo mata agaji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ba aure. Ba da. Babu wani tsayyen namiji. Bani da tabbass. Ya Allah ka taimake ni,” ta rubuta a jikin bidiyonta.

A daidai lokacin wannan rubutun, fiye da mutum 704k ne suka kalli bidiyon yayin da jama’a suka karfafa mata gwiwa.

Kalli Wallafarta a kasa:

Jama’a sun yi martani

hilif :

“Ji mana yake kyakkyawa kawai ki mayar da hankali a kan kanki sannan ki godema abun da kika mallaka…baki gode cewa kina raye ba.”

Beatrice Elechi ta ce:

“Baku san ya mutum yake ji ba duk yadda kayi kokarin mantawa da shi ko boye damuwarka da zaran ka tuna da shi sai ya sa ka kuka.”

Style by misty ta ce:

“Yayata ta cika shekaru 27 sannan ta haifi tagwaye a makon jiya kuma ta mutu yanzu na so ace dama bata yi aure ba balle a kai ga ta haihuwa yanzu ina kewarta.”

Kara karanta wannan

Ke Tauraruwa Ce: Makauniyar ‘Yar Najeriya Ta Doke ‘Yan Mata 18, Ta Ci Gasar Kyau a Bidiyo

Na Fasa Auren: Budurwa Ta Saka Zoben Baikonta a Kasuwa, Zata Siyar N8m

A wani labarin, wata matashiyar budurwa da ta soke aurenta ta saka zoben baikonta da farashin shi ya kai naira miliyan 10.2 a kasuwa.

Bayan ya bayyana karara ba yin auren za a yi ba, sai ta garzaya shafin Facebook domin tallata tsadadden zabon sumfurin Tifanny.

Ta saka farashin zoben na lu’u-lu’u kan $18,500, wanda yayi daidai da naira miliyan 8 wanda yayi kasa da farashin yadda aka siye shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel