"Mijina Sheɗan Ne" Ta Baro Ta Yayin Tattauna Wa da Kawarta Bata San Mijin Na Ji Ba

"Mijina Sheɗan Ne" Ta Baro Ta Yayin Tattauna Wa da Kawarta Bata San Mijin Na Ji Ba

  • Wata mai juna biyu ta shiga ban ɗaki a gidan aurenta domin tattauna wa da kawarta kan Mijinta da kuma maza
  • A kalaman da ta yi da kawarta ta wayar salula, matar tace ba ta cire wa kowa hula ba baki ɗaya maza makaryata ne har da Mijinta
  • Sai dai Matar mai juna biyu bata san cewa Mai gidanta na jin duk abinda take faɗa a waya ba cikin mamaki da kaɗuwa

Wata matar aure mai ɗauke da juna biyu ta bar mijinta cikin kaɗuwa bayan ya saurari magangantun da take da ƙawarta a wayar salula.

Matashiya matar tana tattaunawa da kawarta ne a waya suna baiwa juna labari kan maza, ana haka ne ta tsoma mijinta a ciki.

Matar aure.
"Mijina Sheɗan Ne" Ta Baro Ta Yayin Tattauna Wa da Kawarta Bata San Mijin Na Ji Ba Hoto: foreign_vira/TikTok
Asali: UGC

A cewar Matar, ba ta cire wa kowane namiji hula ba dukkan su ba abun yarda bane domin yaudara ta zama jinin jikinsu kuma ta haɗa harda Sahibinta watau Mijinta.

Kara karanta wannan

Har Masu Zundena Kan Kwasar Bola da Nake yi Sun bi Sahu na: Tsohuwa Mai Shekaru 63

Daɗin daɗawa matar ta misalta Mai gidanta da, "Sheɗan" yayin da take ba da labarin yadda take sa masa ido a ko da yaushe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai Mijin ya shiga tsantsar mamaki yayin da kunnensa ya jiyo masa abinda suke tattauna wa a waya nan take ya shiga tsakani. Tana ganin Mijin cikin sauri ta bar wurin.

Martanin mutane a Soshiyal Midiya

@jeffgoldblum95 tace:

"Ni da babbar ƙawata kenan muna tattauna wa kan abokan rayuwarmu na tsawon lokaci."

@julielubz yace:

"A ko da yaushe kuna kokarin sanya ni murmushi. Nagode ina miki fatan juye abinda ke cikinki lafiya."

@may_bnot_max tace:

"Ina karama haka mamata ke faɗa game da Babana amma sai ta wayance tamkar wasa take saboda ya yi banza da ita."

@maddieforyouuuu

"Wannan dalilin ne ya sa kamata ya yi ki garkame kofa sannan ta tafi can ɗaya bangaren don gudun karsu ji."

Kara karanta wannan

Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

A wani labarin kuma Matashi Ya Gwangwaje Matar Da Ke Bashi Abinci Kyauta Lokacin Da Bai Da Ko Kwabo, Ya Mallaka Mata Gida

Wani matashi ya ba da labarin yadda abubuwa suka sauya a rayuwar wata mai siyar da abinci da ke kyautatawa wani kwastamanta.

Kwastaman ya shafe tsawon lokaci yana karbar abinci kyauta daga wajen mai siyar da abincin har Allah ya buda masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel