Mutane 3 da Aka Gano Ba Su da Laifi Bayan Shafe Shekaru a Gidan Yari

Mutane 3 da Aka Gano Ba Su da Laifi Bayan Shafe Shekaru a Gidan Yari

Akwai labarai da yawa da ake bayar wa na mutanen da aka ayyana ba su da laifi bayan shafe shekaru a magarkama da sunan suna da laifi.

Wani mai shekaru 51, Eddie Bolden, ya kwashi garabasar biliyoyi bayan da ya shafe shekaru 22 a gidan yari bisa kuskure.

Legit.ng ta tattaro labarin wasu mutane uku da wannan iftila'i na yaddda 'shari'a sabanin hankali' ya afka dasu.

Labarin mutanen da aka yanke musu hukunci bisa kuskure
Mutane 3 da Aka Gano Ba Su da Laifi Bayan Shafe Shekaru a Gidan Yari | Hoto: HeadFort foundation, Southbend Tribune
Asali: UGC

1. Otoobong

Otoobong, wani dan Najeriya mai sana'ar gadi kuma kuma kula da lambu, ya sha daurin alkali duk da kuma bai aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidauniyar Headfort dake aikin sa kai wajen dawo da fursunoni kan turba ta bayyana cewa, an tsare matashin ne na tsawon shekara guda da 'yan kai duk kuwa da cewa hukunci aka yi masa kan kuskure.

Kara karanta wannan

Sule Lamido: An Kira Ni Fasto A Arewa Saboda Goodluck Jonathan

Headfort ta naqalto cewa, a shekarar 2020, Otoobang da abokinsa sun magantu kan batun siyar da wata mota ta abokin.

Otoobong ya shaidawa abokinsa cewa, zai taimake shi wajen nemo mai saye, kana ya samo mai saye ya hada shi da abokin.

Bai san da cewa abokinsa da wasu matasa ne suka hada baki wajen sato motar ba, lamarin da ya rufta dashi.

A ranar 24 ga watan Dismaban 2020, 'yan sanda sun bi diddigin motar, suka gano abokin Otoobong da sauran barayin. Aka kama su, amma a garin bincike, aka hada da Otoobong.

A ranar 6 ga watan Agustan 2021, Otoobong da sauran matasan suka gurfana a gaban kotun majistere dake Ogba bisa zargin aikata laifin fashi, daga nan aka tura su magarkama.

Sai dai, bayan shafe shekara guda da watanni shida a gidan yari, an saki Otoobong bayan ayyana shi mara laifi.

2. Eddie Bolden

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

Eddie Bolden ya shaki iskar 'yanci bayan shafe shekaeru 22 a magarkama bisa laifin da bai aikata ba.

An daure Bolden ne a 1994 bisa aikata laifin kisan mutum biyu, sai dai amintattun kotu sun bashi diyyar kudade masu yawa.

Bayan da ya maka birnin Chicago da 'yan sandanta a kotu, amintattun kotu sun ba shi diyyar N9,923,291,764.

A karar da ya shigar, Bolden ya yi ikrarin cewa, an kakaba masa laifin kisan matashi mai shekaru 23 Irving Clayton da kuma mai shekaru 24 Derric Frazier.

Duba da karar da ya shigar, amintattun kotu suka ba da umarnin birnin Chicago ta biya shi diyyar N9,923,291,764 aka kuma umarci wasu jami'an 'yan sanda biyu da su biya shi diyyar N4,042,822.

3. Ola

Ola, wani mazaunin jihar Legas, ya yi zaman gidan kaso na tsawon shekaru takwas bayan yin arba da sojoji a hanyarsa ta dawowa daga wurin aiki.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

A ranar da aka kama shi, Ola ya ga lokacin da sojojin ke bin wasu matasa daga nan aka tsare shi saboda ya ki taimakawa sojoji su kama matasan.

Fusatattun sojojin nan haka suka kwashe shi zuwa barikin soja, daga nan suka mika shi ga 'yan sanda inda aka tsare kafin a zarce dashi kotu, aka kakaba masa laifin fashi.

Har ila yau, gidauniyar Headfort ce ta yada labarin a shafinta na Facebook bayan shiga tsakanin a lamarin tare da kubutar da mutumin da bai ji ba bai gani ba.

Duk da haka dai, ba a bayyana ya samu diyya ba, kuma ya shafe shekaru takwas a magarkama.

Budurwar da Ta Rubuta JAMB Sau 7 Ta Kammala Jami’a, Jama’a Sun Taya Ta Murna

A wani labarin, burin budurwa mai shekaru 27, Mbagwu Amarachi Chilaka ya cika bayan da ta kammala digirinta a jami'ar jiha ta Imo bayan shafe shekaru tana neman gurbin shiga jami'a.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya fadi babban sauyin da zai kawo a aikin 'yan sanda idan ya gaji Buhari

Da take yada hotunan shagalin kammala karatunta a shafin Facebook, Amarachi ta bayyana cewa, ta yi jarrabawar JAMB sau bakwai, ta yi diploma, ta yi karatun sharar fagen shiga jami'a kafin ta samu gurbin karatu.

Bayananta sun bayyana cewa, ta karanta ilimin tarihi da hulda tsakanin kasa da kasa, daga nan ta godewa Allah bisa wannan gata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel