Dirama a Kotu, Wani Saurayi Ya Karbi Kudin Budurwarsa Ya Auti Wata Daban

Dirama a Kotu, Wani Saurayi Ya Karbi Kudin Budurwarsa Ya Auti Wata Daban

  • Yan sanda sun gurfanar da wani matashi, Akeem Bello, a gaban Koliya bisa zargin damfarar budurwarsa miliyan N2m a jihar Ondo
  • Mai gabatar da ƙara yace matar, Olaotan Oladapo, ta samu matsala a mahaifarta saboda yawan zubar da cikin mutumin
  • Alkalin Kotun dake zama a Akure ya ba da umarnin a garkame Akeem har zuwa ranar ci gaba da zaman a watan Nuwamba

Ondo - An gurfanar da wani mutumi ɗan kimanin shekara 30, Akeem Bello, a gaban Kotun Majistire dake Akure, babban birnin jihar Ondo bisa tuhumar ya damafari budurwarsa, Olaotan Oladapo, kudi Miliyan biyu.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an gurfanar da Akeem ne bisa tuhuma biyu, damfara da kuma ƙarya.

Gudumar Kotu.
Dirama a Kotu, Wani Saurayi Ya Karbi Kudin Budurwarsa Ya Auti Wata Daban Hoto: thenation
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa wanda ake zargin ya tafka waɗannan laifuka ne a tsakanin watan Maris zuwa Disamban wannan shekarar da muke ciki.

Kara karanta wannan

Mun Bar Wa Allah Ya Zaba Mana Shugabn Kasa a 2023, Wani Babban Sarki Ya Faɗa Wa Atiku Ido-da-Ido

An ce Akeem Bello ya fara soyayya da matar da ya damafara ne tun a shekarar 2018.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗan sanda mai shigar da ƙara, Insufekta A. Ajeniwa, ya faɗa wa Kotun cewa wanda ake zargin ya fara yaudarar budurwar ne a 2020 ta hanyar amfani da kuɗaɗen da take turo masa daga ƙasar waje a harkokin dake gabansa.

Insufekta Ajeniwa ya gaya wa mai shari'a cewa ana zargin Akeem ya yi amfanin da kuɗin wurin auren wata budurwa ta daban.

Ɗan sandan ya kara da cewa mahaifar wacce ke ƙara ta lalace sakamakon yawan zubar da cikin wanda ake zargi.

Yace laifin da ya aikata ya saɓa wa dokar sashi na 383 da 421,390 (b da c) dake ƙunshe a kundin dokokin manyan laifuka na jihar Ondo 2006.

Wane mataki Kotun ta ɗauka?

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Bayan sauraron ƙarar, Alkalin Kotun mai shari'a C.M Akinwumi, ya umarci a garkame wanda ake zargi a gidan gyaran halin Olokuta.

Daga nan kuma ya ɗage shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba, 2022 domin ci gaba da sauraron ƙorafin.

A wani labarin kuma Babban Malamin Jami'a A Nasarawa Da Yayansa Sun Yi Wa Ɗaliba Tsirara Don Ta Yi Fada Da Ƴarsa Kan Saurayi

Yan sanda a Jihar Nasarawa sun kama wani babban malami a Jami'ar Tarayya da ke Lafiya, Dr Fred Ekpe Ayokhai, kan zargin cin zarafi.

Wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna malamin da yayansa yayin da suke lakadawa wata yarinya duka kan cewa ta doki yarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel