Babban Malamin Jami'a A Nasarawa Da Yayansa Sun Yi Wa Ɗaliba Tsirara Don Ta Yi Fada Da Ƴarsa Kan Saurayi

Babban Malamin Jami'a A Nasarawa Da Yayansa Sun Yi Wa Ɗaliba Tsirara Don Ta Yi Fada Da Ƴarsa Kan Saurayi

  • Yan sanda a Jihar Nasarawa sun kama wani babban malami a Jami'ar Tarayya da ke Lafiya, Dr Fred Ekpe Ayokhai, kan zargin cin zarafi
  • Wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna malamin da yayansa yayin da suke lakadawa wata yarinya duka kan cewa ta doki yarsa
  • Bayanai da bidiyo da suka bayyana a soshiyal midiya sun nuna cewa rikici ne ya shiga tsakanin yar malamin, Emmanuella da kawarta, Blessing, kan saurayin kawar

Nasarawa - Yan Najeriya a dandalin sada zumunta a Twitter, suna ta sukar wani malamin jami'ar tarayya da ke Lafia, Jihar Nasarawa, Dr Fred Ekpe Ayokhai, saboda cin zarafin wata yarinya da aka ce sun yi fada da yarsa kan namiji, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

A bidiyon da aka wallafa a Twitter, an hangi Fred Ayokhai da yaransa suna duka wata yarinya da ake ce sunanta Blessing Mathias har da tube ta.

Malami da ake zargi da dukan daliba
Babban Malamin Jami'a A Nasarawa Da Yayansa Sun Yi Wa Daliba Tsirara Don Ta Yi Fada Da Yarsa Kan Saurayi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kafin su yi mata dukan, Blessing ta yi wa yar malamin jami'ar, Emmanuella duka saboda kokarin kwace mata saurayinta.

Sunyi fadan ne bayan ta gano cewa Emmanuella tana da lambar saurayinta a wayarta, kuma ta ci cire lambar.

An rahoto cewa Blessing ta tattaro kawayenta don su yi wa Emmanuella duka. Bidiyon ya nuna ta tana marin Emmanuella, tana ce mata ta cire lambar saurayin.

Emmanuella da iyayenta sun dawo daukan fansa

Bayan yan kwanaki, Emmanuella da mahaifinta, Ayokhai, da yan uwanta sun lakada wa Blessing duka.

A bidiyon da ya bazu a intanet, an ga Ayokhai ya yi amfani da almakashi ya yanke rigar Blessing bayan sun dauke ta a mota daga gida sun kai ta wani wuri da ba a sani ba, suna ta dukanta.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Bidiyon ya nuna yadda suka rika yi mata duka da sanduna da rassan bishiya yayin da ta ke ta bada hakuri da neman afuwa daga Blessing.

Mun kama malamin da yarsa - Kakakin yan sanda

Benjamin Hundeyin, kakakin yan sandan jihar Legas, a wani karin bayani da ya yi ranar Asabar ya ce rundunar yan sandan Nasarawa na bincike kan lamarin.

A wani rubutu a Twitter, yan sandan na Nasarawa sun ce an kama mutum biyu kan zargi da hannu a lamarin.

Ya ce ana cigaba da bincike yayin da ake neman sauran wadanda ke da hannun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel